Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Olivier Giroud: Zai ci gaba da taka leda a Chelsea
Olivier Giroud na daf da saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Chelsea har zuwa karshen kakar 2021.
A watan Janairu aka sa ran dan wasan tawagar Faransa zai bar Stamford Bridge, bayan da ya buga wa Chelsea wasa biyar, kuma saura wata shida kwantiraginsa ya kare.
An danganta shi da cewar zai koma Inter Milan a lokacin da Chelsea ta yi ta neman mai cin kwallo da zai maye gurbinsa koda ta sayar da shi.
Sai dai kuma Chelsea ta ci gaba da sa shi a wasanni bayan da Tammy Abraham ya yi rauni a Janairu, kuma Giroud ya taka rawa gani a lokacin inda ya ci kwallo biyu a wasa hudu a Premier.
Giroud ya koma Stamford Bridge daga Arsenal a watan Janairun 2018 kan fam miliyan 18 a yarjejeniyar wata 18 a lokacin.
Daga nan ya tsawaita yarjejenyarsa zuwa kakar tamaula daya a watan Mayun 2019.