Coronavirus: Wane hali manyan gasar kwallon Turai ke ciki?

An wallafa

An dakatar da yawancin gasar kwallon kafa a nahiyar Turai saboda yaduwar da cutar korona ke cigaba da yi.

Nan take aka tsayar da wasanni a Ingila, sai dai ana sa ran ranar Juma'a kungiyoyin da ke buga gasar Premier za su yi taro ranar Juma'a don nemo mafita, da kyar ne idan nan kusa zai koma buga tamaula, musamman a manyan gasar Turai inda ya rage wa wasu kasashe wasannin tara su karkare kakar bana.

Shin wane hali sauran gasar kasashen Turai ke ciki?

Bundesliga – wasu kungiyoyin sun fara atisaye

A makon jiya wWasu kungiyoyin da ke buga gasar Bundesliga suka yi atisaye, tun bayan da aka dakatar da gasar.

Bayern Munich na daga cikin kungiyoyin Jamus da suka yi atisaye kuma sun dauki matakan kauce yada cutar korona inda suka dinga motsa jiki tare da yin tazara a tsakaninsu a mataki na rukunin mutum biyar.

An dakatar da gasar Bundesliga a ranar 13 ga watan Maris da ake sa ran ci gaba da wasanni ranar 30 ga watan Afirilu, kuma saura wasa tara a karkare kakar bana, inda Bayern ce ke kan gaba a teburi.

A ranar Talata an samu karin yawan mutanen da suka kamu da annobar, fiye da wadanda ta harba a mako ukun da suka gabata, bayan da cutar ta dan lafa a baya.

La Liga – late May return is best-case scenario

Watakila a ci gaba da wasannin La Liga ranar 28 ga watan Mayu idan komai ya koma yadda ya kamata, in ji shugaban gudanar da gasar La Liga, Javier Tebas.

Bayan da aka dakatar da gasar Sipaniya a cikin watan Maris, Barcelona ce ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid, yayin da sauran wasanni 11 a karkare wasannin shekarar nan.

Spaniya daya ce daga kasashen da aka fi samun wadanda suka kamu da cutar korona, sai dai yanzu ana samun raguwar wadanda ke kamuwa da annobar.

Kawo yanzu an sa dokar hana fita waje a Spaniya, bayan da aka umarci kowa ya zauna agida.

Ligue 1 – Watakil a ci gaba da wasanni cikin watan Yuni

Watakila a ci gaba da gasar Ligue a Faransa ranar 1 ko 3 ko kuma 17 ga watan Yuni kamar yadda jaridar L’Equipe ta ce.

Kamar yadda aka ce idan har an ci gaba da wasannin ranar 17 ga watan Yuni, kungiyoyi za su dinga buga wasa duk bayan kwana uku, wanda hakan zai iya sa a kammala kakar bana ranar 25 ga watan Yuli kenan, kuma za a samu lokacin buga wasannin cike gurbi da wadanda za su bar buga gasar bana zuwa 2 ga watan Agusta.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya tsawaita dokar ci gaba da zama a gida a kasar zuwa 11 ga watan Mayu.

Kasar ce ta uku a nahiyar Turai da aka samu wadanda suka mutu da yawa sakamakon cutar korona.

Serie A – ana sa ran ci gaba da wasanni cikin watan Mayu

Hukumar kwallon kafar Italiya na shirin gwajin cutar korona ga 'yan wasan da ke buga gasar kafin kasar ta amince a ci gaba da wasannin a watan Mayu.

An tsayar da gasar Serie A ranar 9 ga watan Maris a lokacin saura wasanni 12 a kammala kakar bana da kuma kwantan wasa hudu, yayin da Juventus ce ke kan gaba a teburi da maki daya tsakaninta da Lazio.

Italiya ce kan gaba a Turai da cutar korona ta yi wa illa da mutane da dama suka mutu mai yawan 'yan kwallon da suka kamu da annobar.