Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a kara shekarun cancantar buga kwallo a Olympic
Watakila hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta kara shekarrun 'yan kwallon da suka cancanta buga gasar Olympic daga 23 zuwa 24.
Fifa na fatan daukar wannan matakin a lokacin Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci a 2021, wasannin da ya kamata a yi a 2020, amma annobar coronavirus ta sa aka dage gasar ta bana.
Hakan na nufin duk 'yan kwallon da aka haifa kafin ko kuma ranar 1 ga watan Janairun 1997 za su iya buga wasannin badi.
Sai dai kuma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.
Ana sa ran gudanar da bikin gasar Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci daga 23 ga watan Yulin 2021.
Haka kuma an amince da zabar 'yan kwallo uku da shekarunsu ya haura zuwa Olympic da su ci gaba da buga wa kasa tamaula idan ta gayyace su.
Haka kuma hukumar kwallon kafa ta duniya ta amince da dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa na maza da na mata na mambobinta a 2020, sakamakon annobar da ake fama da ita.