Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ozil ba zai bar Arsenal ba, Arrizabalaga zai bar Chelsea
Golan Spain Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, ya ce a shirye yake ya bar Chelsea a wannan bazara bayan an fara ajiye shi benci. (Sun)
Shi ma Arrizabalaga yana shirin barin Stamford Bridge bayan kocin kungiyar Frank Lampard ya soma ajiye golan a benci. (Mail)
Sai dai Lampard ya ce Arrizabalaga yana da damar daukar matakin da zai fisher shi a kungiyar. (Sky Sports)
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya aika da wakilai domin sa ido kan dan wasan Fiorentina mai shekara 22 Federico Chiesa, wanda ya kai fam milyan £60. (Mail)
Wakilin dan wasan Jamus Mesut Ozil, mai shekara 31, ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiyar na Arsenal ba zai bar kulub din ba idan kwangilarsa ta kare watan Yunin 2021. (inews)
Burin Arsenal na zubin sabbin 'yan wasa ya gamu da cikas bayan fitar da kulob din daga Europa League. (Sun)
Dan wasan tsakiya na Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, ya nuna ba ya son barin kulob din duk da sha'warsa da Manchester United ke yi masa. (Express)
Amma kocin Aston Villa Dean Smith ba ya da tabbacin ko Grealish zai zauna, ko da kuwa sun lashe kofin kalubale a wasan da za su kece raini da Manchester City ranar Lahadi. (Mirror)
Tsohon kocin Aston Villa Alex McLeish ya bayyana cewa Manchester United ta kusan sayen dan wasan kan fam miliyan £200,000 a 2012. (Mail)
Wakilin dan wasan tsakiyar RB Leipzig mai shekara 28 dan kasar Sweden Emil Forsberg ya ce ba mamaki kocin Tottenham Jose Mourinho yana sha'awarsa a tawagarsa. (Expressen - in Swedish)
Tsohon kaftin din Ingila David Beckham ya ce zai yi maraba da dan wasan Portugal da Juventus Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, da kuma abokin hamayyarsa na Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 32, a sabuwar kungiyarsa Inter Miami. (ESPN)
Babu tabbas ko za a bayyana Liverpool a matsayin wadda ta lashe Premier a bana idan har an dakatar da wasannin gasar saboda cutar corona. (Telegraph)
Leicester City na daf da karbo aron dan wasan Faransa Arnaud Lusamba, mai shekara 23, da zarar kwantaraginsa a Nice ta kare a karshen kakar wasa ta bana.
West Ham za ta bari dan wasan Ingila mai shekara 21, Nathan Holland ya bar kungiyar a kan £2m a karshen kakar wasan bana. (Football Insider)