Zan lashe zinare 5 a damben festival na Najeriya

An wallafa

Sarkin shirya wasan dambe na Najeriya, Mamman Bashar Danliti ya ce zai lashe zinare biyar a wasannin damben festival da za a yi a 2020.

Jihar Edo ce za ta karbi bakuncin wasannin karo na 20 da za a yi tsakanin ranar 20 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afirilu.

Ana kuma sa ran lashe zinare 3,000 a wasa 36 da jihohin kasar 36 za su kece raini har da babban birnin tarayya Abuja.

Mammam Bashar shi ne zai ja ragamar jihar Kano a wasannin gargajiya da suka hada da dambe da langa da kuma kokawa.

A wasannin da aka yi a Abuja gasa ta 19, jihar Kano ta lashe zinare uku, inda Bahagon Sanin Kurna da Bahagon Shagon 'Yan Sanda da kuma Abdurrazak Ebola suka zama gwanaye.

Sai Ali Kanin Bello da ya ci azurka a nauyin ajin kilo 85, bayan da ya yi rashion nasara a wasan karshe a hannun Mai Takwasara da ya wakilci jihar Edo.

'Yan wasan da za su wakilci jihar Kano a damben festival:

Ajin nauyi kilo 55 Bahagon Sanin Kurna

Ajin nauyi kilo 65 Autan Dan Bunza

Ajin nauyi kilo 75 Bahagon Shagon 'Yan Sanda

Ajin nauyi kilo 85 Ali Kanin Bello

Ajin nauyi kilo 100 Abdurrazak Ebola