West Ham United ta dauki Tomas Soucek

An wallafa

West Ham United ta amince da daukar Tomas Soucek daga Slavia Prague kan fam miliyan 13.

Kocin West Ham, David Moyes ya tabbatar da cinikin ya kuma ce ana duba koshin lafiyar Soucek, mai shekara 24, kan ya rattaba hannu kan yarjejeniya.

Moyes ya ce dan kwallon na tawagar Jamhuriyar Czech, yana da kwarewar da yake bukata, zai kuma taimakawa kungiyar.

Moyes, wanda ya maye gurbin Manuel Pellegrini ranar 30 ga watan Disamba ya ce West Ham tana zawarcin wani dan wasa mai tsaron baya daga gefe.

Soucek, ya ci kwallo 10 a wasa 19 da ya buga wa Slavia Prague a kakar bana.

West Ham tana ta 17 a kasan teburin gasar Premier ta bana.