Arsenal za ta ninkawa Martinelli albashi sau uku, Chelsea na neman Cavani

Willian Jose

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool na harin dan wasan gaban Real Socieded dan asalin Brazil William Jose mai shekara 28, ana sa ran zai ziyarci Landan don kammala tattaunawa, in ji jaridar. (AS)

Chelsea ta bayyana sha'awarta ta daukar dan wasan gaban PSG Edison Cavani dan kasar Uruguay mai shekara 32, sai dai zai je ne don buga kwantragin aro kamar yadda jaridar wasanni ta (Times - subscription required) ta rawaito.

(Guardian) ta rawaito cewa mahaifin Cavani ya ce akwai yiwuwar dan nasa ya bugawa Atletico Madrid wasa matsawar kulub din zai iya cimma yarjejeniya da PSG.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG na neman Euro miliyan biyar daga wurin Arsenal don sayar mata da dan wasanta Layvin Kurzawa a wannan watan, a kakar nan ne kwantraginsa za ta kare da kungiyar, in ji (Telegraph).

Real Madrid na shirin sake sayar da dan wasanta Gareth Bale ga tsohuwar kungiyarsa ta Tottenham, sai dai kungiyar na fargabar yadda cinikin zai kasance. (Telegraph)

Kulub din Leicester na dab da cimma yarjejeniya da dan wasan bayan Southampton Jannik Vestegaard mai shekara 27, bayan mika tayin Euro miliyan 17 a kan dan wasan na Denmark kamar yadda (Sun) ta ruwaito.

Akwai yiwuwar cewa Bayern Munich ba za ta ki amincewa da bukatar Barcelona ta rike Philippe Coutinho din-din ba kasancewar yana buga kwantragin aro tare da ita (Bild, via Mirror).

Kungiyoyin Primier shida ne ke neman daukar dan wasan bayan Tottenham Danny Rose mai shekara 29 a wannan watan in ji (Sky Sports).

An daf da ninninkawa dan wasan gaban Arsenal Gabriel Martinelli albashin sa har sau uku domin yi masa danna kirjin sake rattaba hannu don kasancewa a kungiyar har nan da wasu shekaru masu tsayi sosai. (Football London)

Jaridar Mail ta ce tuni kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fara hararo dan wasan domin dauke shi.

An danganta kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da daukar dan wasan bayan Athletico Paranaense wato Bruno Guimaraes mai shekara 22, sai dai a yanzu ya shirya tsaf domin jonewa da Lyon ta Faransa a cewar jaridar L'Equipe, via Mirror.

Westham na son dawo da tsohon dan wasan ta Dimitiri Peyet mai shekara 32 da ya bar kungiyar a 2017 don komawa Marseille, kamar yadda jaridar ta rawaito.