Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An hana kungiyoyin Iran buga wasannin AFC Champions League a cikin kasar
Kungiyoyi hudu na kwallon kafa a kasar Iran da ke buga gasar Zakarun Asiya ta AFC Champions League sun ce ba za su buga wasannin gasar ba idan har ba za su karbi bakuncin wasannin ba, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Mehr.
Hukumar kwallon kafar Iran ta ce hukumar AFC ta hana kungiyoyin Iran buga wasanninsu na gida a cikin Iran.
AFC ta ce tana son wasannin da kungiyoyin za su yi a buga su a wajen kasar.
Wannan yunkurin ya zo ne yayin da dangantaka take kara tsami tsakanin Iran da Amurka.
Hukumar kwallon kafar Iran ta ce za ta sanar da "matsayarta" a cikin 'yan kwanaki "masu zuwa".
Iran tana da kulob hudu a gasar AFC Champions League - Persepolis da Esteghlal da Sepahan da Shahr Khodro kuma a yau Asabar ake sa ran za a tuntube su.
Sai dai Mehr ya ce kungiyoyin za su mika wasika ga AFC domin bayyana cewa za su fice daga gasar idan ba za su buga wasan gida a Iran ba.