Ghana ta kori masu horas da 'yan wasan kasar

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta kasar Ghana (GFA) ta cire dukkan masu horas da kungiyoyin wasa na kasar.

An yi wannan sanarwar ne da yammacin ranar Alhamis abin da ya kawo karshen zango na biyu na Kwesi Appiah a matsayin kocin babbar kungiyar wasan kwallon kafar kasar.

A cikin sanarwar, hukumar ta tabbatar da "rushe masu kula da kungiyoyin kwallon kafa na kasa da gaggawa".

Wannan guguwa ta yi awon gaba da Kwesi Appiah da sauran masu ba shi shawara da suka hada da Richard Kingson da Charles Akunnor da Stephen Appiah.