Dejan Kulusevski: Juventus ta sayi dan wasan Sweden

An wallafa

Kungiyar Juventus ta sayi dan wasan tsakiyar Sweden Dejan Kulusevski daga Atalanta a kan yarjejeniyar yuro miliyan 35 (fam miliyan 29.7).

Dan kwallon mai shekara 19 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da rabi da kungiyar Serie A, amma zai koma Parma a matsayin aro har zuwa karshen kaka.

Kulusevski ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara daya da Parma a watan Yulin 2019 kuma ya zura kwallaye 17.

Ya fara taka wa Sweden leda ne a watan Nuwamba a wasan neman shiga gasar Euro 2020.

Kudin da za a biya Kulusevski zai iya kai wa yuro miliyan 44m (fam miliyan 37), amma hakan ya danganta da yadda dan kwallon ya cika wasu sharudda.