An bukaci Fifa ta kai Sepp Blatter da Platini kara

SappBlatter da Michel Platini

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sapp Blatter Tsohon shugaban Fifa da tsohon shugaban Uefa Michel Platini
An wallafa

An bukaci Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa da ta kaddamar da wani bincike na musamman kan tsohon shugabanta Sepp Blatter da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa Michel Platini domin su dawo da kudi sama da Fan miliyan daya da rabi.

Blatter mai shekara 83, ya sahale wa Platini wasu kudi da suka kai kimanin Swiss francs miliyan biyu, daidai da fan miliyan 1.5 a ranar 18 ga watan Junairun 2011, bayan mako biyu aka tura kudin zuwa asusun Platini daga asusun Fifa.

Amma babu wani dalili da ya nuna cewa za a biyan kudin a wannan tsukukun, sai dai idan kyauta aka ba shi.

Mambobin kwamitin gudanarwar Fifa duka bakinsu ya hadu kan a dawo da kudin ba tare da bata lokaci ba gami da wasu karin kudin ruwa da Fifa ke nema da kuma karin kudin tara domin ladabtarwa.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC a watan Yuli, Blatter ya ce shi "mutum ne mai gaskiya" ya kuma fara daukar matakan shari'a don ganin Fifa ta dawo masa da agogunansa 60.

Shekara 17 da Blatter ya kwashe yana shugabantar Fifa sun kare ne bayan zarginsa da badalar kudi a 2015, wanda ya janyo aka dakatar da shi na tsawon shekara shida daga shiga harkokin kwallon kafa.

Ya yi zargin ana yada bayanan karya a kansa kan wasu kudi da ya karba bayan dawowa daga gasar cin Kofin Duniya ta 2014.

Fifa ta ce matsayar Blatter ta yanzu ta ci karo da dokokin da ya samar lokacin da yake ofis.

Blatter da kuma Platini mai shekara 64 dukansu sun sha musanta aikata ba daidai ba.