Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Arsenal na ci gaba da nutsewa
Arsenal na ci gaba da nutsewa a teburin Premier bayan Brighton ta casa ta har gida 1-2 a wasan Premier mako na 15.
Wannan ce kakar wasa mafi muni ga Arsenal cikin shekara 42 - yanzu haka maki 10 ne tsakaninta da gurbin shiga gasar Champions League kuma ta 10 a teburi.
Shi ne wasa na farko da kocin rikon kwarya Freddie Ljungberg ya jagoranta a filin wasa na Emirates, inda shi kuma Alexandre Lacazette ya buga wasa na 100 kuma shi ne ya farke wa Arsenal kwallon farko a wasan.
Adam Webster ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal din tun kafin hutun rabin lokaci.
Gunners ba su ji dadi ba yayin da aka soke kwallon da David Luiz ya ci a minti na 64 sakamakon satar gida da ya yi, in ji na'urar VAR.
Neal Maupay ne ya ci wa Brighton kwallo ta biyu da taimakon Aaron Mooy.
Bayan tashi daga wasan koci Ljungberg ya ce ya fahimci cewa rashin kwarin gwiwa ne ke damun 'yan wasansa.
"Abin da yake damun kowanne koci kenan, zan yi aiki kan hakan kuma zan yi magana da su ('yan wasa) domin dawo masu da kwarin gwiwarsu," Ljungberg ya fada.
Game da matsalar tsaro da suke fuskanta a bangaren baya, Ljungberg ya ce:
"Tabbas abu ne da a koyaushe za mu ci gaba da tattaunawa a kai. Muna bukatar mu kara kokari."