Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Liverpool ta sha da kyar a hannun Brighton
Jagorar Premier Liverpool ta ci gaba da zama a saman teburin gasar amma wannan karon da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester City, bayan ta sha da kyar a hannun Brighton da ci 2-1.
Kare jini biri jini aka yi a wasan, hasali ma Brighton ta fi rike kwallo da kashi 55%, Liverpool kuma ta rike kashi 45%.
Dan wasan bayan Liverpool Virgil van Diijk ne gwarzon wasan sakamakon kwallo biyu da ya ci a minti na 18 da kuma 24.
An kori mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker a minti na 76 bisa taba kwallo da ya yi da hannu a wajen yadi na 18. Minti biyu bayan haka kuma Dunk ya farke wa Brighton kwallo daya.
Haka Liverppool ta ci gaba da kare gida har lafari ya tashi wasan.
Idan Leicester City ta ci wasanta a gobe Lahadi za ta koma ta biyu a teburin kuma ta rage tazarar zuwa maki takwas maimakon 11 da ta bayar a yanzu.