'Nuno Espirito Santo ne zai maye gurbin Emery'

An wallafa

'Yar manuniya ta nuna cewa kocin Wolves Nuno Espirito Santo ne kan gaba cikin wadanda ake sa ran za su maye gurbin kocin Arsenal Unai Emery. (Mail)

Ma'aikatan Arsenal sun yi amannar cewa za a kori Emery, amma ana sa ran zai tsaya har wasan da za su yi na Europa League tsakaninsu da Eintracht Frankfurt a ranar Alhamis. (Goal)

Sai dai kuma idan har Arsenal ta yi rashin nasara kan Frankfurt, da Norwich City a ranar Lahadi, to Emery zai rasa aikinsa. (Express)

A shirye Barcelona da Real Madrid suke don sayo dan wasan gaban Arsenal mai shekara 30, Pierre-Emerick Aubameyang. (Mirror)

Kungiyar Barcelona ce kan gaba wajen kokarin sayo Aubameyang. (Star)

Everton za ta iya duba yiwuwar maye gurbin kocinta Marco Silva da kocin Flamengo Jorge Jesus, wanda ya jagoranci nasarar kungiyar Copa Libertadores ta Brazil. (Telegraph)

Everton na fuskantar fafatawa daga West Ham don tsira da David Moyes a matsayin sabon kocinsu. (Mirror)

Manchester United sun yi amannar su ne na gaba-gaba wajen sayo dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 19 Jadon Sancho, a badi. (Telegraph)

Mamallakin kungiyar Manchester United Ed Woodard ya ce "an samu bambancin ra'ayi kan dan wasa daya ko biyu" tsakanin kungiyar da tsohon kocinta Jose Mourinho. (Mirror)

Sabuwar kwantiragin dan wasan gaban Ingila Raheem Sterling da Manchester City za ta iya sa wa dan wasan mai shekara 24 ya dinga samun fiye da fam 350,000 da Kevin de Bruyne ke dauka duk mako. (Sky Sports)

Manchester United da Tottenham da kuma Liverpool na daga cikin kungiyoyin da ke gasar neman dan wasan Peterborough mai shekara 17 Ricky-Jade Jones. (Mail)

Bayern Munich ba su da ra'ayin daukar tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino, kungiyar za ta bar kocinta Hansi Flick ya ci gaba har zuwa karshen kakar nan. (Goal)

Har yanzu kocin Real Madrid Zinedine Zidane yana tsananin son sayo dan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba mai shekara 26, duk da cewa mamallakin kungiyar Florentino Perez ya fi son a dauko dan wasan Tottenham Christian Eriksen mai shekara 27, ko Fabian Ruiz mai shekara 23 na Napoli. (Mirror)