Mourinho na son dawo da Bale Tottenham

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Sabon kocin Tottenham Jose Mourinho zai yi kokarin sayo tsohon dan wasan kungiyar Gareth Bale mai shekara 30 daga Real Madrid, saboda yadda ya so ya sayi dan wasan tun lokacin da yake kocin Manchester United. (AS - in Spanish)

Mourinho yana kuma son sayo dan wasan tsakiya na kasar Portugal Bruno Fernandes mai shekara 25, da dan wasan Benfica Ruben Dias mai shekara 22, da kuma dan wasan tsakiya na Manchester United Nemanja Matic mai shekara 31. (Independent)

Tsohon dan wasan baya na Arsenal Martin Keown ya yi amannar cewa ya kamata tsohuwar kungiyar tasa ta dauki tsohon kocin Tottenham, Mauricio Pochettino. (Mail)

A shirye Barcelona da Bayern Munich suke su sayo Mauricio Pochettino. (Sun)

Har yanzu dan wasan gaban kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang mai shekara 30 bai sabunta kwantiraginsa da Arsenal ba, saboda yana jiran Barcelona. (Mirror)

Real Madrid ta toshe hanyar ficewar Bale daga kungiyar a watan Janairu, duk da wani hoto da ya dauka a gaban wata tuta da aka rubuta'Wales. Golf. Madrid. a jiki, a yayin da yake international duty. (Marca)

Manchester United na duba yiwuwar sayo dan wasan Roma Edin Dzeko mai shekara 33 a watan Janairu. (ESPN)

Dan wasan tsakiyar Ingila James Maddison mai shekara 22 yana duba yiwuwar kulla yarjejeniya da Leicester, duk da matukar sha'awar sayensa da Manchester United ke yi. (Manchester Evening News)

Wakilin Zlatan Ibrahimovic Mino Raiola, ya gana da kungiyar AC Milan kan batun komawar dan wasan kungiyar. (Corriere dello Sport - in Italian)

Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta kara nuna sha'awarta kan dan wasan gaban Red Bull Salzburg, Erling Haaland mai shekara 19, bayan da suka gayyaci mahaifin dan wasan wanda tsohon dan wasan Leeds ne Alf-Inge Haaland, domin ya ziyarci wajen atisayensu. (Sport Bild, via Metro)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na shirin sayo Haaland. (Mail)

Juventus za ta yi kokarin gamsar da dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe mai shekara 20, don shan gaban Real Madrid wajen sayo dan wasan ya koma kungiyar ta Serie A daga Paris St-Germain. (Tuttosport, via Sky Sports)

Kudurin Inter Milan na karbo dan wasan Chelsea da Faransa Olivier Giroud mai shekara 33, yana iya samun cikas daga bukatun dan wasan. (La Gazzetta dello Sport, via Mail)

Aston Villa na son sayen dan wasan gaba a watan Janairu, kuma suna sa ido ne a Italiya. (The Athletic, via Birmingham Mail)

Everton za ta samu damar sayen dan wasan AC Milan Krzysztof Piatek mai shekara 24, a wata yarjejeniyar musaya da za ta sa Moise Kean mai shekara 19 ya koma Milan. (Sport Witness)