Courtois ya yi wasa 200 kwallo ba ta shiga ragarsa ba

An wallafa

Ranar Lahadi tawagar kwallon kafa ta Belgium ta je ta doke ta Kazakhtan 2-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020.

A wasan ne mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Courtois ya yi fafatawa ta 200 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba.

Cikin lissafin har da wanda ya tsare ragar kungiyar Genk da Atletico Madrid da Chelsea da kuma Real Madrid.

Tawagar ta Belgium ta lashe dukkan wasanninta na neman shiga gasar cin kofin Turai, kuma kwallo daya ne ya shiga ragarta, bayan da ta ci 30.

Courtois ya tsare raga a tawagar Belgium sau bakwai kwallo bai shiga ragarsa ba, rabonda a ci golan tun wadda Deny Cheryshev ya yi a wasan zagayen farko a cikin rukuni a wasan neman shiga gasar Turan.

  • Wasannin da Courtois ya yi gola kwallo bai shiga ragarsa ba
  • Wasa 154 a Chelsea, karawa 58 kwallo bai shiga raga ba
  • Wasa 154 a Atletico Madrid, fafatawa 76 kwallo bai shiga ragarsa ba
  • Wasa 45 a Genk, gumurzu 14 kwallo bai shiga ragarsa ba
  • Wasa 43 a Real Madrid, sau 12 kwallo bai shiga ragarsa ba
  • Wasa 78 a Belgium, fafatawa 40 kwallo bai shiga ragarsa ba