Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal za ta ba da aron Ozil, Mandzukic zai koma Man Utd
Jaridar (Mirror) ta ruwaito cewa Arsenal na son bayar da aron dan wasan tsakiyarta, Mesut Ozil, a watan Janairu - ko da kuwa za su rage farashin sayar da dan wasan mai shekara 30 ne.
Kocin Inter Milan Antonio Conte na shaukin ganin ya sayo dan wasan Manchester United dan kasar Serbia Nemanja Matic, mai shekara 31, in ji jaridar (Calciomercato).
Manchester United za ta iya sayen dan wasan Juventus da Croatia Mario Mandzukic, mai shekara 33, a watan Janairu, wanda suka so saya a bazara. Da alama Jeventus za su so a biya su £9m, kuma ba za a rage albashin £4.5m da ake bai wa Mandzukic ba, a cewar (Goal.com)
Mandzukic ya kammala tattaunwar da yake yi da Al Rayyan don haka ba zai koma kungiyar da ke Qatar ba, in ji (Goal.com)
Dan wasan Manchester United dan kasar Scotland Scott McTominay, mai shekara 22, ya ce zai ci gaba da yin hakuri da kocinsa Ole Gunnar Solskjaer. (Mirror)
Solskjaer ya tabbatar da cewa babban abin da zai bai wa muhummanci a lokacin musayar 'yan wasa shi ne sayen dan wasan gaba da kuma inganta masu buga wasa na gaba ganin cewa kulob din Manchester United ya gaza cin kwallo fiye da daya a wasa 17 cikin 20 da suka fafata. (Telegraph)
PSV Eindhoven na son aron dan wasan Manchester United dan kasar Netherlands mai buga wasa a rukunin 'yan kasa da shekara 21 Tahith Chong a watan Janairu. (Sun)
Dan wasan tsakiya na Liverpool James Milner yana shekarar karshe a kwantaragin da ya sanya hannu a kulob din ko da yake koci Jurgen Klopp ya yi amannar cewa dan wasan mai shekara 33 zai tsawaita zamansa a kulob din. (Express)
Dan wasan Napoli dan kasar Belgium Dries Mertens, mai shekara 32, ya shirya tsaf domin barin kulob din, in ji (Calciomercato)
Kocin Arsenal Unai Emery ya musanta cewa bambacin yare tsakaninsa da 'yan wasansa yana hana shi isar da sako gare su - ko da yake ya kwatanta jin turancinsa da cewa kashi shida ne cikin goma. (Mirror)
Tsohon dan wasan tsakiya na ArsenalEmmanuel Petit ya garagadi Emery bisa yawan sauya 'yan wasansa. (Sun)
Kocin Stoke da ke shan matsin-lamba Nathan Jones ya dage cewa yana da kwarin gwiwa kan rawar da yake takawa kuma shi ne mutumin da zai iya cire wa kulob din kitse daga wuta. (Stoke Sentinel)
Dan wasan Bayern Munichmai shekara 30 Ivan Perisic, wanda Inter Milan ta karbi aron sa, ya ce yana daf da komawa Manchester United lokacin da Jose Mourinho ke jagorancin kulob din. (Athletic, via Express)