Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko an rage hamayya tsakanin United da Arsenal?
Arsenal za ta ziyarci Old Trafford domin karawa da manchester United a karashen wasan mako na bakwai a gasar cin kofin Premier da za su fafata ranar Litinin.
Arsenal tana mataki na takwas da maki 11, ita kuwa United ce ta 11 da makinta takwas kacal.
A baya da zarar kungiyoyin biyu za su kara a kan yi adawa mai zafi ta yadda tun kan a shiga fili ake ta cece-kuce tsakanin magoya baya.
Sai dai watakila 'yan wasan United, Anthony Martial da kuma Marcus Rashford ba za su buga wasan ba, hakan zai sa Mason Greenwood, mai shekara 17, ya fara buga wasan farko a Premier.
Haka ma da kyar ne idan Paul Pogba zai buga gumurzun sakamakon raunin da ya yi a karawa da Rochdale a gasar Caraboa, amma Luke Shaw ya yi atisaye.
Dan kwallon Arsenal mai wasan gaba Alexandre Lacazette ba zai buga wasan ba, sakamakon jinya, amma Dinos Mavropanos ya warke sarai.
Shima Emile Smith Rowe na jinya, sai dai Rob Holding da Hector Bellerin da kuma Kieran Tierney duk suna cikin koshin lafiya.
Arsenal ba ta yi nasara a gidan United a manyan wasa 12 da ta buga ba, sannan karawa uku ta ci daga 27 da ta ziyarci Old Trafford a gasar Premier.
Wasa ukun da ta yi nasara duk da ci daya mai ban haushi ne, kuma Ole Gunnar Solskjaer ya buga wa United a lokacin yana wasa da Arsenal ta doke United a Old Trafford.
Arsenal na fatan yin nasara a kan United wasa biyu a jere a karon farko tun bayan 2006-07.
A kakar bara sau uku Manchester United da Arsenal suka kara a tsakaninsu, inda suka yi 2-2 a gasar Premier a Old Trafford ranar 5 ga watan Disambar 2018.
Sun kuma kara a FA Cup ranar 25 ga watan Janairu, inda Manchester United ta yi nasarar doke Arsenal da ci 3-1.
Haka kuma sun hadu a gasar Premier a gidan Arsenal wato Emirates, inda Arsenal ta doke United da ci 2-0 ranar 10 ga watan Maris, 2019.