Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
FIFA The Best Award: Messi da Ronaldo da Van Dijk na takara
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Virgil van Dijk ne aka bayyana sunayensu a matsayin wadanda ke takarar lashe gwarzon shekara na kwallon maza wato Best Fifa Football Awards - sai dai ko wane ne zai lashe wannan kyautar?
Shin ko yaya za ku iya bambance gwarzon dan wasa cikin gwaraza uku, wadanda kowannensu ke da kambu iri-iri a lalitarsa, idan aka ba ku dama?
BBC ta nemi wasu daga cikin marubuta harkokin wasanni Andy West da Phil McNulty da su yi fashin baki kan kowanne daga cikin 'yan wasan.
Sai dai a cikin wadandan 'yan wasan guda uku wa kuke ganin zai lashe gwarzon dan wasan FIFA na bana.
Za ku iya zabar guda daga cikin su a kasa.