Real Madrid vs Sevilla: Benzema ya ceci Zidane

An wallafa

Real madrid ta kai bantenta a wasan La Liga mako na biyar bayan da ta sha da kyar a hannun Sevilla, godiya ta musamman ga Kareem Benzema wanda ya ceci tawagar ta Zinedine Zidane.

Nasarar tana nufin Real din ta bi sahun Atletic Bilbao wajen darewa saman teburi kowaccensu da maki 11, inda suka bar babbar abokiyar hamayya Barcelona a mataki na takwas.

Wannan ce rashin nasara ta farko ga tsohon kocin Real Madird Julen Lopetegui da kungiyarsa ta Sevilla a La Liga ta bana, wadanda yanzu suka koma mataki na biyar.

Kareem Benzema ya ci kwallo daya tilon da Madrid ta dogara da ita ne a minti na 64 tare da taimakon Dani Carvajal.

Duk da irin matsin lambar da mai horarwa Zinedine Zidane ke fuskanta a Bernabeu kungiyar tasa ta kai gwauro ta kai mari a filin wasa na Estadio Ramon Sanchez Pizjuan.

Hakan na nufin sun farfado daga abin kunyar da ya faru a tsakiyar makon jiya a birnin Paris, duk da cewa akwai wasan adawar birnin Madrid tsakaninta da Atletico Madrid Asabar mai zuwa.

Sai dai kafin haka za ta fafata da Osasuna a ranar Laraba a wasan mako na 6.

Sakamakon wasannin Lahadi:

Sakamakon wasannin Asabar: