Gareth Bale ya hana Madrid jin kunya

Gareh Bale

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta tashi 2-2 a gidan Villareal a wasan mako na uku a gasar cin kofin La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

Minti 12 da fara tamaula, Villareal ta ci kwallon farko ta hannun Gerard Moreno, sai dai Gareth Bale ya farke ta tun kan aje hutu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Villareal ta kara na biyu ta hannun Moi Gomez, kuma Gareth Bale ne dai ya kara farke ta.

Sai dai kuma Real ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Gareth Bale jan kati daf da za a tashi daga fafatawar.

Bale dan kwallon tawagar Wales ya zama na biyu a 'yan wasan Madrid, wanda ya ci kwallo biyu a wasa sannan aka bashi jan kati a karawar, bayan Cristiano Ronaldo.

Wannan sakamakon ya kai Real mataki na biyar a teburin La Liga, ita kuwa Villareal tana ta 16 a wasannin shekarar nan.

Ko a kakar bara kungiyoyin 2-2 suka taashi a gasar La Laliga, sai dai Real ta yi nasara da ci 3-2 a Santiago Bernabeu.

Real za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na hudu ranar 14 ga watan Satumba, Villareal kuwa gidan Leganes za ta je a ranar.

Yadda kungiyoyin suka murza-leda

Villareal Real Madrid

Asalin hoton, BBC Sport