Van Dijk ne gwarzon dan kwallon Turai na bana

Virgil van Dijk

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan Liverpool, Virgil van Dirk shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar Turai na bana.

Dan wasan mai tsaron baya ya taimakawa Liverpool ta doke Tottenham a wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai da aka kammala.

Van Dijk mai shekara 28 ya yi nasara ne a kan Lionel Messi na Barcelona da tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai taka-leda a Juventus.

Dan wasan ya zama kashin bayan Liverpool tun lokacin da ya koma Anfield da taka-leda daga Southampton a Janairun 2018 kan fam miliyan 75 a matsayin mafi tsada a lokacin.

Van Dijk dan kwallon tawagar Netherlands ya taimakawa kasarsa ta kai wasan karshe a UEFA Nations League a bana, inda ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Portugal.

Haka kuma an bayyana 'yar Ingila, Lucy Bronze a matsayin gwarzuwar macen da babu kamarta a fagen tamaula a Turai a bana.

Mai tsaron baya Bronze ta yi nasara ne kan wadanda ta yi takara da su da ya hada da Ada Hegerberg da kuma Amandine Henry.

Bronze ita ce macen farko daga Ingila da ta lashe kyautar da masu horar da tamaula mata ke yi da wasu 'yan jarida ke zaba.