Juventus na son Suarez, Ribery ya koma Fiorentina

An wallafa

Tsohon dan wasan gaban Bayern Munich Franck Ribery ya koma Fiorentina mai buga gasar Serie A ta Italiya a kyauta.

Ribery mai shekara 36 ya kasance ba tare da wata yarjejeniya ba bayan shafe shekara 12 a gasar Bundesliga tare da Bayern.

Ya koma Bayern din ne a shekarar 2007, inda ya buga wasanni 425 tare da lashe kofunan Bundesliga da kuma na Zakarun Turai wato Champions League a 2013.

Kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya tana neman Marcos Rojo na Manchester United mai shekara 29 a matsyain aro, in ji Manchester Evening News.

Juventus tana son dan wasan Barcelona dan kasar Uruguay Luis Suarez, mai shekara 32, idan Neymar ya koma Barcelona daga Paris St-Germain, a cewar jaridar Sun.

Sabon dan wasan gaban Real Madrid Luka Jovic dan kasar Serbia ka iya tafiya AC Milan a matsayin aro wata biyu kacal bayan zuwansa Madrid kan fan miliyan 62, in ji Gazzetta.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce "zai yi ritaya nan da shekara biyu zuwa uku" - bayan kwantiraginsa ya kare a kungiyar a shekarar 2022, kamar yadda kafar yada labarai ta Gianluca di Marzio ta ruwaito.

Kungiyoyin Manchester City da Tottenham da kuma Arsenal suna zawarcin dan wasan kungiyar Rennes, Eduardo Camavinga mai shekara 16, in ji rahoton jaridar Mail.

Arsenal tana son kulla yarjejeniyar shekara biyar da dan wasan Faransa Matteo Guendouzi dan shekara 20, inda za a ninka albashinsa zuwa fan 70,000 a duk mako, in ji jaridar Mail.