Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Joao Cancelo: Man City ta sayi dan wasan baya Cancelo daga Juventus
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kammala sayen dan wasan bayan dan kasar Potugal Joao Cancelo daga Juventus a kan fam miliyan 60.
A yarjejeniyar da aka cimma, dan wasan baya na City Danilo mai shekara 28, shi kuma zai koma Juventus a kan fam miliyan 34.
Cancelo, mai shekara 25 ya sanya hannu kan yarjejeniyar buga wa City kwallo ne har zuwa bazarar 2025, kuma ya kasance dan wasa na uku da kulob din ya saya bayan Angelino da Rodri.
Cancelo ya ce "City kulob ne mai daraja, da yake da manaja mai basira, kuma ina farin cikin kasancewa a nan."
"Duk abubuwan kulob din suna burge ni, daga filin wasa na Etihad zuwa yanayin wasansu," in ji Cancelo.
Ya kara da cewa "ina kuma fatan bunkasa wasana, in ci kofi, kuma na yi imani cewa zan iya cimma burina a nan, don haka a yanzu ina dokin a fara sabuwar kakar wasanni domin in gwada kaina a gasar firimiya," a cewarsa.
Cancelo, wanda kuma zai iya buga gaba ya koma Juventus ne daga Valencia a kan fam miliyan 34 a 2019, bayan kammala kakar shekarar, yayin da yake buga wa Valencia din wasa a matsayin aro daga Inter Milan.
Daraktan kwallon kafa na City Txiki Begiristain ya ce "Joao dan wasa ne kwararre, kuma dan wasan baya mai hazaka da ke iya kai kora, wanda zai ringa keta tsaron abokan karawarmu ta bangren dama."
"Mun gamsu da yadda yake samun ci gaba, kuma ba ma shakkun cewa tauraruwarsa za ta ci gaba da haskawa a Manchester," a cewar daraktan.
Ya ce, dan wasan ya cika sharuddan irin 'yan wasan da muke nema a Machaster City. Nan gaba zai kara zama wani gwarzo.
A shekarar 2017 Man City ta sayi Danilo daga Real Madrid a kan fan miliyan 26.5, kuma ya taba shiga cikin taurarin gasar wasanni 22, a wasa 60 da ya buga.
Dan wasan dan Brazil, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar taka leda a Juventus ta tsawon shekara biyar, na cikin 'yan wasan da City ta dauki kofi da su sau biyu a karkashin Guardiola, sai dai ba a fiye saka shi a cikin 11 na farko ba.