Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gianluigi Buffon ya amince ya sake koma wa Juventus
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
Tsohon golan Italiya Gianluigi Buffon ya amince ya sake koma Juventus bayan shafe kaka daya kacal a Paris St-Germain.
Buffon, mai shekara 41, ya shafe shekara 17 a Turin kafin ya koma Paris St-Germain a kakar da ta gabata.
A watan da ya gabata ne ya sanar da cewa zai bar PSG, kuma BBC ta fahimci cewa za a gwada lafiyarsa a Juventus ranar Alhamis.
Golan, wanda ya buga wa Italiya wasa sau 176, yana daga cikin 'yan wasan da suka fi samun nasara a fagen tamaula.
Ba ya ga gasar cin kofin duniya da ya lashe a 2006, Buffon ya lashe gasar Serie A sau tara da Coppa Italia hudu. Ya kuma lashe gasar Lig ta Faransa a kakar da ta gabata.
Buffon zai zamo dan wasa na uku da Juventus ta dauka kyauta a bana bayan da ta dauki Aaron Ramsey daga Arsenal da kuma Adrien Rabiot daga PSG.