Madrid ko Barca - ina Neymar zai koma? Man Utd na tsaka mai wuya

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan gaba na Brazil Neymar na ci gaba da neman komawa Barcelona kuma ba shi da niyyar sake bugawa Paris St-Germain kwallo, a cewar jaridar (Sport - in Spanish).

Sai dai rahotanni sun ce Real Madrid ta taya Neymar, inda ta ce za ta bai wa PSG Yuro miliyan 130, tare dan wasan Wales Gareth Bale, ko kuma na Colombia James Rodriguez, in ji (Mundo Deportivo - in Spanish).

Atletico Madrid na dab da kammala cinikin dan wasan gaba na Benfica Joao Felix, kan Yuro miliyan 120, wanda hakan ke nufin Manchester United za ta rasa matashin dan kwallon na Portugal, kamar yadda jaridar (Evening Standard) ta ce.

Yunkurin kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na sauya fasalin kulob din na tsaka mai wuya bayan da kungiyoyin da United ke neman 'yan wasansu ke nuna takaicin yadda take yi musu tayin wulakanci, in ji (Evening Standard).

A gefe guda kuma ana hasashen Manchester City za ta kasa Manchester United a rige-rigen da suke yi na daukar dan wasan baya na Leicester City Harry Maguire kan fan miliyan 65, a cewar (Star).

Dan wasan tsakiya na Leicester City James Maddison, mai shekara 22, ya nemi a bashi dama ya gana da kocin United Solskjaer, wanda yake matukar bukatar ya sayi matashin dan wasan na Ingila, in ji (Star).

Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Solskjaer na san gyra Manchester United bayan da ta tabarbare

Dan wasan Atletico Madrid Rodri ya zabi ya koma Manchester City maimakon Bayern Munich, inda ake sa ran za a saye shi fam miliyan 62, a cewar (Kicker - in German).

Shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu ya nanata aniyarsa ta rike dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 22, a Nou Camp, duk da cewa Liverpool na neman dan kwallon, kamar yadda Daily Mirror ta rawaito.

Har ila yau dai Liverpool na duba yiwuwar taya dan wasan baya na Real Betis Junior Firpo, mai shekara 22, domin maye gurbin Alberto Moreno, in ji (Mirror).

Juventus na fatan sayen dan wasan Paris St-Germain Adrien Rabiot, wanda kwantiraginsa ta kare a karshen kakar da aka kammala, a cewar (Goal).