Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea za ta dauko Lampard, Man U na son Rakitic
Juventus na nazarin dauko kocin Chelsea Maurizio Sarri domin ya maye gurbin Massimiliano Allegri, wanda ya bar kungiyar. (Sky Sports)
Chelsea ta fara nazarin dauko kocin Derby Frank Lampard tsohon dan wasanta domin ba shi aikin horar da 'yan wasan idan har Sarri ya koma Juve. (Daily Mirror, via Sky Sport Italia)
Chelsea ba za ta iya hana Sarri barin kulob din ba idan har Juventus ta amince za ta biya shi fam miliyan biyar domin dawo da shi Italiya. (Telegraph)
Manchester United tana son karbo Ivan Rakitic, mai shekara 31, kuma Barcelona ta nuna sha'awar sayar da dan wasan tsakiyar na Croatia. (Daily Record)
Golan Spain da Manchester United David de Gea, mai shekara 28, ya ki amincewa ya sabunta kwantaraginsa idan har kwangilarsa ta kawo karshe a badi. (Sun)
Manchester United za ta ba Paul Pogba mukamin kaftin domin janyo hankalinsa ya ci gaba da taka leda a Old Trafford. (ESPN)
Arsenal za ta dauko golan Dynamo Dresden da Jamus Markus Schubert, mai shekara 20, domin maye gurbin Petr Cech bayan ya yi ritaya. (Bild - in German)
Fiye da magoya bayan Real Madrid 330, 000 suka kada kuri'a kan rawar da 'yan wasan kulob din suka taka a kakar 2018-19 inda kashi 92 suka ce Gareth Bale ya gaza. (Marca)
Tottenham ta kawo karshen bukatar da take yi wa dan wasan Newscastle United Wilfied Zaha, mai shekara 26, bayan saka farashin darajarsa fam miliyan 100. (Evening Standard)