Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zakarun Turai: Kafar Ajax daya ta kai wasan karshe
Tottenham ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Ajax a wasan farko na daf da karshe a gasar Zakarun Turai da suka fafata ranar Talata.
Ajax ta ci kwallon ne ta hannun Donny van de Beek a minti na 15 da fara tamaula.
Kungiyar ta Holland za ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar 8 ga watan Mayu.
Ita dai Ajax ta lashe kofin Zakarun Turai na Champions League karo hudu, ita kuwa Tottenham wannan ne karon farko da ta kawo wannan matakin.
Ajax ce ta fitar da Real Madrid da kuma Juventus a wasannin gasar bana, ita kuwa Tottenham ce ta doke Borussia Dortmund da Manchester City.
Ajax ta amfana da hutun da hukumar kwallon Netherland ta bayar a karshen mako, domin kungiyar ta shirya fafatawa da Tottenham cikin natsuwa.
Liverpool za ta ziyarci Barcelona a daya wasan daf da karshe ranar Laraba, kuma duk wadda ta yi nasara a fafatawa biyun za ta fuskanci ko Ajax ko kuma Tottenham.