Real Madrid ta sake dauko Zinedine Zidane

An wallafa

Zinedine Zidane ya dawo aikin horar da Real Madrid, watani 10 bayan ya ajiye aikinsa.

Zidane zai maye gurbin Santiago Solari ne wanda ya jagoranci kulob din na kusan tsawon wata biyar.

Tsohon dan wasan na Madrid mai shekara 46, ya bar horar da kulob din bayan lashe gasar Zakarun Turai ta Champions Leage karo uku a jere.

Yanzu haka Madrid suna mataki na uku a teburin La Liga, tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona wadda ke saman teburi da maki 63.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ce gwarzon koci a duniya ya dawo aikin horar da Real Madrid.

Real ta raba gari da Solari bayan nasarar da ta yi ci 4-1 a wasa da Real Valladolid ranar Lahadi, wannan kuma na zuwa bayan kashin da Madrid ta a hannun Ajax ta Netherlands a gasar Zakarun Turai da kuma yadda Barcelona ta fitar da ita Copa del Ray da kuma doke ta a La Liga.