Neymar na kwadayin Real Madrid

An wallafa

Dan wasan Paris St Germain, Neymar ya haskaka cewar zai iya komawa Real Madrid da taka-leda.

Dan wasan tawagar Brazil, wanda aka saya da tsada fiye da kowa a tarihin kwallon kafar duniya na yin jinyar raunin da ya ji a yatsan kafarsa ranar 23 ga watan Janairu.

An dade ana alakanta Neymar tsohon dan kwallon Barcelona da cewar zai koma wasa Real Madrid tun bayan da PSG ta saye shi a shekarar 2013.

Neymar ya shaidawa kafar watsa labarai ta talabijin, channel Globo ''Nan gaba, komai zai iya faruwa.''

Ya kara da cewar ''Ku kwantar da hankulanku, ban ce zan koma Real Madrid ba, kowa ya san cewar na cika burina da na taka-leda a Barcelona.''

Neymar ya ce Real babbar kungiyar tamaula ce a duniya, kuma kowanne dan wasa na son ya buga mata kwallo, ''amma yanzu ina Paris, ina kuma jin dadi zama a birnin.''

Neymar ba zai buga wa PSG wasa na biyu da kungiyar za ta karbi bakuncin Manchester United a ranar Laraba ba, bayan da ta United 2-0 a Old Tarfford a karawar farko.

Psg na sa ran dan kwallon zai dawo fagen fama a cikin watan Afirilu.