Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Uefa ta dakatar da Sergio Ramos buga wasanni biyu
Hukumar kwallon kafar nahiyar Turai Uefa ta dakatar da dan wasan Real Madrid Sergio Ramos daga buga wasanni biyu bayan ya aikata laifi da gangan don ya samu katin gargadi a wasansu da Ajax a gasar Zakarun Turai.
A wasan da Madrid ta doke Ajax da ci 2-1, Ramos ya yi wa Kasper Dolberg keta a minti na 89, wanda hakan yake nufin an dakatar da shi daga buga wasan gaba.
Dan wasan bayan Spain din ya shaida wa manema labarai cewa "zai yi karya idan ya ce bai nemi hakan da gangan ba".
Hukumar Uefa ta yi bincike game da batun kuma ta hana shi buga karin wasa guda saboda ya nemi katin gargadi da gangan.
Bayan da Ramos ya karbi katin gargadin, hakan yana nufin ya rage yiwuwar kin buga wani babban wasa da ke gaba.
Sai dai saboda wannan hukunci na hukumar Uefa, idan Real Madrid ta kai matakin wasan gab da na karshe, Ramos ba zai buga wasan ba.