Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Antonio Conte ya raina ni — Mourinho
Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce yana ganin kocin Chelsea Antonio Conte ya "raina" shi bayan shugabannin biyu sun yi sa-in-sa.
Ranar Talata Conte ya ce ba zai taba mantawa da takaddamar da ke tsakaninsa da abokin hamayyarsa ba.
Sai dai ranar Juma'a Mourinho ya ce: "Ina tsammanin idan mutum ya ci zarafin wani, ya kamata ya ba shi hakuri idan ba haka ba ya raina shi shi ya sa zai yi shiru.
"Karon farko da [Conte] ya zage ni na yi masa raddin da na sani cewa ya yi masa kuna."
Ya kara da cewa: "Ya sake zagi na karo na biyu, amma yanzu na sauya. A gare ni, hakan raini ne."
Wannan dai wani yunkuri ne da Mourinho ke yi na ganin an kawo karshen ce-ce-ku-cen da ke tsakaninsu.