Lafiya Zinariya: Ko kun san matan da suka fi samun sanko?
Danna hoton da ke sama domin sauraren shirin:
Kungiyar likitocin fata ta Amurka da Canada wato, AAD, ta ce mata na samun sanko a tsakar ka, kuma wannan matsala ta fi yawa a tsakanin mata bakaken-fata.
Kungiyar ta bayyana cewa baya ga su, maza na samunsa kuma matsalar ta shafi mutane gaba daya ba tare da bambancin launin fata ko asali ba.
Sai dai matsala ce mai sarkakiya, wadda a cewar kungiyar an kasa gano ainihin abin da ke kawo sanko dake farawa daga tsakiyar kai.
Haka kuma miliyoyin mata a duniya na fuskantar wani nau'in matsalar, wadda cikar gashi ke raguwa, kuma ya fara cinyewa daga gefen kunne, in ji kungiyar.
Sai dai ta bayar da shawarar cewa yana da duk wanda ya ga alamun zubewar gashi to ya je ya ga likitar fata tun da wuri, domin a wasu lokutan idan an yi magani gashi na sake tsurowa.
Amma idan lokaci ya kure sanko ya girma ya fata tushen gashi to gashin baya tsurowa da kansa.
Wasu daga cikin hanyoyin maganin matsalar cinyewar gashi sun hada da yin amfani da wasu mayuka domin sa gashin ya sake tsuro ko kuma yin dashen gashi.












