Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC 100 Women 2021: Su waye sunayensu suka shiga shirin Mata 100 na BBC 2021?
BBC ta bayyana sunayen mata 100 da suka yi abubuwan bajinta daga faɗin duniya a shekarar 2021.
Daga cikinsu akwai Malala Yousafzai, mafi ƙanƙantar shekarun da ta taɓa karɓar lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, da kuma fira minista mace ta farko a ƙasar Samoa wato Fiamē Naomi Mata'afa, da Farfesa Heidi J Larson, wacce take jagorantar shirin riga-kafi na Vaccine Confidence Project, da kuma marubuciyar litattafai ƴar Najeriya Chimamanda Ngozi Adichie.
Mata daga Pakistan ne suka mamaye kusa rabin jerin na bana, waɗanda wasunsu aka sauya musu suna kuma ba a wallafa hotunansu ba saboda tsaro.
Farfaɗowar Taliban a watan Agustan 2021 ya sauya rayuwar miliyoyin ƴan Afghanistan - inda aka haramta wa mata yin karatun sakandare, aka rusa ma'aikatar harkokin mata ta ƙasar, sannan aka hana mata da dama zuwa aiki.
An zaɓo mata 100 na bana ne duba da irin hazaƙa da jarumta da nasarorinsu a daidai lokacin da suke inganta rayuwawarsu.
Ga jerin sunayen mata 100 masu labaran da ke cike da ƙarfafa gwiwa na BBC na shekarar 2021 da kuma irin sauyin da suke kawowa a duniya.
Ta yaya aka zaɓo mata 100n?
Tawagar sashen mata 100 ta BBC ce ta tattaro sunayen matan ta hanyar shawarwarin da abokan aiki daga bangarorin BBC daban-daban suka gabatar.
Mun nemi sunayen matan da suka mamaye kanun labarai ko suka yi tasiri a wasu labaran da suka faru a cikin wata 12 da suka gabata, da ma waɗanda suke da wasu labaran ƙarfafa gwiwa, ko suka cimma wani muhimmin abu a cikin al'ummominsu ko da ba su mamaye kanun labarai ba.
An zabi matan na bana ne duba da taken bikin na bana - matan da suke ƙoƙarin seta abin da ya sauya, kan irin rawar da suka taka ta farfaɗo da duniya bayan annobar cutar korona wacce ta sauya kan irin yadda muke rayuwa.
Sannan sai da aka duba wakilcin yankunan da suka fito saboda gudun nuna bambanci, kafin a kammala tattara sunayen waɗanda aka zaɓa.
A bana, shirin Mata 100 na BBC sun ɗauki matakin da ba su taɓa irinsa ba, inda rabin matan suka fito daga ƙasa ɗaya - Afghanistan.
Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun mamaye kanun labarai kuma sun sa miliyoyin ƴan Afghanistan suna tababa a kan makomarsu, yayin da ƙungiyoyin kare hakkokin mata suke magana kan fagabar da suke da ita ta cewa akwai yiwuwar a daƙile ƴancin mata a ƙarƙashin mulkin Taliban.
A yayin da muke sadaukar da rabin sunayen wannan shiri ga matan da suka fito daga ƙasa ɗaya, mun nuna yadda aka tursasa wa waɗannan matan ɓacewa daga jama'a, da kuma yaɗa muryoyin waɗanda aka tursasa wa rufe musu baki waɗanda a yanzu suna cikin ƴan Afghanistan ɗin da ke zama a ƙasashen waje.
Ba a bayyana sunayen wasu daga cikin mata ƴan Afghanistan din da aka zaɓa ba, domin kare su da iyalansu, kuma da izininsu aka yi hakan, ta bin ƙa'idojin aiki na BBC da dokokin kariya.
Waɗanda suka yi aikin
Wadanda suka shirya suka tace: Valeria Perasso, Amelia Butterly, Lara Owen, Georgina Pearce, Kawoon Khamoosh, Haniya Ali, Mark Shea.
Editar BBC 100 Women: Claire Williams.
Shugabannin aikin: Paul Sargeant, Philippa Joy, Ana Lucía González.
Wadanda suka tsara: Ayu Widyaningsih Idjaja, Alexander Ivanov,Debie Loizou, Zoe Bartholemew.
Zane: Jilla Dastmalchi.
Hakkin mallakar hotuna: Fadil Berisha, Gerwin Polu/Talamua Media, Gregg DeGuire/Getty Images, Netflix, Manny Jefferson, University College London (UCL), Zuno Photography, Brian Mwando, S.H. Raihan, CAMGEW, Ferhat Elik, Chloé Desnoyers, Reuters, Boudewijn Bollmann, Imran Karim Khattak/RedOn Films, Patrick Dowse, Kate Warren, Sherridon Poyer, Fondo Semillas, Magnificent Lenses Limited, Darcy Hemley, Ray Ryan Photography Tuam, Carla Policella/Ministry of Women, Gender and Diversity (Argentina), Matías Salazar, Acumen Pictures, Mercia Windwaai, Carlos Orsi/Questão de Ciência, Yuriy Ogarkov, Setiz/@setiz, Made Antarawan, Peter Hurley, Jason Bell, University of Sheffield Hallam, Caroline Mardok, Emad Mankusa, David M. Benett/Getty, East West Institute Flickr Gallery, Rashed Lovaan, Abdullah Rafiq, RFH, Jenny Lewis, Ram Parkash Studio, Oslo Freedom Forum, Kiana Hayeri/Malala Fund, Fatima Hasani, Nasrin Raofi, Mohammad Anwar Danishyar, Sophie Sheinwald, Payez Jahanbeen, James Batten.
Mene ne shirin Mata 100?
BShirin Mata 100 Na BBC sunaye ne na mata 100 masu faɗa a ji ko wadanda suka yi wasu ayyuka da ke sa ƙwarin gwiwa daga fadin duniya, da ake zaba a kowace shekara.
Muna ƙirƙirar shirye-shirye da dogwayen maƙaloli da hirarraki a kan rayuwars - labaran da ke sa muata agaba-gaba.