Lafiya Zinariya: Jarirai na kamuwa da cutukan da uwa ta dauka wajen jima'i
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin:
Wannan ci gaban na makon da ya gabata ne, kuma an tattauna ne da wata kwararriyar likitar mata Dr Mairo Mandara.
Wasu hanyoyi uku da mata masu juna biyu ke iya yada wasu cututtuka zuwa ga jariransu su ne, a ciki da lokacin haihuwa da kuma yayin shayarwa, in ji likitoci.
Wadannan cututtuka suna da dama, amma wasu daga cikinsu su ne, ciwon hanta, cutar sanyi, cutar Tetanus, cutar karambau da kuma cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya.
Kungiyar kwararrun likitocin mata ta Amurka, ACOG, ta bayyana cutar HIV da cewa tana daya daga cikin cututtukan da uwa ke yadawa zuwa ga danta.
Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake daukar kwayar cutar HIV dai shi ne ta hanyar jini.
Haka kuma da zarar kwayar cutar ta shiga jini sai ta mamaye kwayoyin halittar da ake kira CD4, a likitance.
Wadannan kwayoyin halittun su ne jiga-jigan garkuwar jikin dan adam.
Saboda haka, sai garkuwar ta yi rauni kuma jiki ya kasa yaki da kwayoyin cututtukan da za su kama mutum.
ACOG ta ce akwai wasu hanyoyin wadanda idan mace mai ciki kuma mai HIV ta bisu, to akwai yiyuwar kashi 99 cikin dari ba za ta yada cutar ga jaririnta ba.
Wasu na baya da za ku so
Na farko shi ne shan magungunan yaki da cutar kamar yadda likita ya rubuta, a lokacin da mace ke da ciki.
Hanya ta biyu kuma ita ce a yi mata tiyata a cire dan maimakon haihuwa da kanta, idan gwajin da aka yi ya nuna cewa cutar ta HIV ta yi karfi sosai a jikin mai juna biyun.
Mataki na uku kuma shi ne mai cikin ta sha magungunan yaki da cutar a lokacin nakuda da kuma a wajen haihuwa kamar yadda ya dace.
Hanya ta hudu ita ce ta bai wa jaririn magungunan yaki da cutar bayan haihuwarsa. In ji ACOG
Sai hanya ta karshe ita ce, kada uwa ta shayar da danta nono, domin za ta iya yada cutar ga jaririnta ta hanyar shayarwa.
Kungiyar kwararrun likitocin matan ta ce bin wadannan hanyoyin zai yi matukar rage hadarin yada cutar HIV daga uwa zuwa ga jaririnta.












