Ku San Malamanku tare da Sheikh Jalo Jalingo

An wallafa

Shahararren malamin Musuluncin nan, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Muhammad Jalingo ya ce ya fara karatu ne domin ya ƙware a harshen Larabci da kuma adabi ba wai karatun Fiƙihu da sauransu ba kafin daga baya ƙaddara ta sauya masa layi.

Sheikh Jalingo ya bayyana hakan ne a shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, yana mai cewa tun yana yaro yake sha'awar nahawun Larabci da waƙe-waƙensu.

An haifi malamin a garin Jacci da ke Jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 1960.

Neman ilimi

Sheikh Jalo Jalingo ya fara karatu ytun yana ƙarami a hannun babban yayansa a ƙauyensu, inda ya fara tun daga karatun babbaƙu har zuwa ya sauke Alƙur'ani mai girma.

Ya samu shiga Jami'ar Bayero ta Kano, inda ya fara karanta fannin harshen Hausa da darussan Musulunci da Larabci, kafin daga baya ya bari ya tafi Jami'ar Musulunci Madina da ke Saudiyya.

A jami'ar Madina malamin ya kammala digirinsa na farko da na biyu da na uku bayan ya isa Saudiyya a 2004.

Kafin tafiyar tasa, malam ya nemi gurbi a jami'o'i da suka haɗa da jami'ar Musulunci ta Nijar da wata jami'a a Chadi da kuma Jihar Legas.

Kazalika, Sheikh ya je birnin Accra na Ghana domin koyon harshen Ingilishi sannan ya shafe kusan shekara guda a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Fannin da Sheikh Jalingo ya fi sha'awa

Malamin ya ce akwai fannonin ilimi da ya fi ƙarewa a kai da kuma wanda ya fi sha'awa.

"Fannin da na fi sha'awa tun tasowata shi ne Larabci da nahawu da waƙe-waƙe," in ji malamin.

Ya ce har sai da ya je jami'a sannan ya fahimci cewa abin da zai karanta kenan. "Tun ba na jin daɗin abin kuma har na aba da shi".

Sana'a

Lokacin da Malam Jalingo bai wuce shekara 17 ba, 'yan uwansa sun yi yunƙurin su yi masa aure amma ya ce ba ya so kuma ya mayar da hankali kan neman sana'a.

Ya koyi sana'ar kafinta na tsawon shekara biyu har ma ya fara ayyuka tare da ci gaba da neman ilimi.

Abin farin ciki da baƙin ciki

Malam Ibrahim Jalingo ya ce babban abin farin ciki da ba zai taɓa mantawa da shi ba shi ne lokacin da ya samu gurbin karatu a Jami'ar Madina.

"Ina tunawa wata rana ina Ghana, da na farka wajen ƙarfe 1:00 na dare sai na ga ɓarawo ya sace mani komfuta (laptop).

"Na yi baƙin ciki sosai. Ba zan iya mantawa da wannan dare ba. Na dinga kiran abokaina a wannan loakci kamar wanda ya haukace. Na kasa haƙuri."

Iyali

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, malam yana da mata huɗu da kuma 'ya'ya 36 rayayyu - maza 21 da kuma mata 15.

"Wataƙila ma akwai wasu masu zuwa kwanan nan," in ji malam.