May Day: Kalubalen da ma'aikatan gwamnati suke fuskanta a Najeriya

Bayanan sautiMay Day: Kalubalen da ma'aikatan gwamnati suke fuskanta a Najeriya
An wallafa

Ku latsa sama don sauraro:

Yau ce ranar ma’aikata ta duniya, wata rana da aka kebe a duk ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara domin tuna wa da yanayin da harkar kwadago ke ciki.

A wannan shekara, ma’aikata a Najeriya sun fuskanci kalubale iri-iri kama daga kora daga aiki da fafutukar neman ganin an aiwatar da biyan albashi mafi karanta da kuma tsadar rayuwa.

Albarkacin wannan rana, Usman Minjibir ya tattauna da shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Comrade Ayuba Wabba inda ya fara da bayani kan maudu’in bikin ranar ta wannan shekara.