Gane Mini Hanya 24/04/2021: Faston da ya gina masallaci a Adamawa

Bayanan sautiGane Mini Hanya 24/04/2021: Faston da ya gina masallaci a Adamawa
An wallafa

Ku latsa sama don sauraro:

A makon da ya gaba ta ne a wani abu da ba a saba gani ba a kasa irin Najeriya, aka bude wani masallaci a hukumance wanda wani malamin addinin kirista ya gina wa 'yan gudun hijira mabiya addinin Musulunci domin gudanar da ibada.

Faston na cocin katolika wanda shi ne shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN a jihar Adamawa, Most Reverend Stephen Dami Mamza, ya ce ya gina masallacin ne wanda ya cinye sama da Naira miliyan biyar da rabi domin ba Musulmi daga cikin 'yan gudun hijiran damar gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba.

A filin mu na Gane Mini Hanya na wannan makon, abokin aikin mu Salihu Adamu Usman ya kasance daya daga cikin wadanda suka halarci sallar farko a masallacin, sannan ya hada mana rahoto na musamman.