Nupur Sharma: Kalaman ɓatanci kan Annabi Muhammad sun 'ɓata' tsakanin Indiya da ƙasashen Larabawa

    • Marubuci, Daga Vikas Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
  • An wallafa

Ala tilas Indiya ta bai wa ƙasashen Musulmai da take alaƙa da su haƙuri, bayan wasu kalaman ɓatanci da suka jawo da ce-ce-ku-ce da wasu manyan jami'an gwamnatinta suka yi a kan Annabi Muhammad.

Mai magana da yawun jam'iyya mai mulki ta Hindu nationalist Bharatiya Janata Party (BJP), Nupur Sharma ce ta yi kalaman a wata muhawara da aka yi a talabijin a watan da ya gabata.

Shi ma Naveen Jindal, shugaban sashen yaɗa labarai na jam'iyyar ya sake wallafa saƙo kan batun a Tuwita.

Kalaman Ms Sharma sun harzuƙa al'ummar Musulmai da suka kasance marasa rinjaye a ƙasar, abin da ya jawo zanga-zanga a wasu jihohin.

BBC ba za ta maimaita kalaman da Ms Sharma ta yi ba saboda tsaurin su.

Jami'an sun bai wa al'umma haƙuri kuma jam'iyyar ta dakatar da Ms Sharma tare da korar Mr Jindal.

A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar ta ce: "BJP ta yi tur da duk wasu kalaman ɓatanci kan wasu mutane ko wani addini. Sannan BJP ba ta yarda da duk wata aƙida ta cin mutuncin wani addini ba. Babu ruwan BJP da aƙidar waɗannan mutanen."

Masu suka sun ce kalaman Ms Sharma da Mr Jindal sun nuna irin tsantsar rabuwar kan da ke tsakanin mabiya addinai da ake fama da shi tsawon shekaru a ƙasar.

Ana samun ƙaruwar kalaman ƙiyayya da kai hare-hare kan Musulmai tun bayan da BJP ta hau mulkin ƙasar a 2014.

Ƙwararru sun ƙara da cewa martanin da BJP ta yi bai isa ba, bayan da lamarin da ake ganin na cikin gida ne ya rikiɗe zuwa na ƙasashen waje - Kuwait da Qatar da Iran sun yi wa jakadunsu kiranye don nuna rashin jin daɗinsu a ranar Lahadi.

Ita ma Saudiyya a ranar Litinin ta yi tur da kalaman. Qatar kuwa cewa ta yi tana tsammanin Indiya ta ba ta haƙuri.

Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta ce: "Ƙin ɗaukar matakai kan irin waɗannan kalamai na ƙin jinin Musulunci na zama wani babban haɗari ga kariyar haƙƙin ɗan adam, kuma zai iya jawo wariya, lamarin da ka iya kawo tashin hankali da ƙiyayya."

Saudiyya ita ma a tata sanarwar ta yi amfani da kalamai masu ƙarfi. "Ma'aikatar harkokin waje ta yi tur da Allah-wadai da kalaman mai magana da yawun jam'iyyar BJP."

Jakadiyar Indiya a Qatar Deepak Mittal, ta ce kalaman da wasu masu son tayar da zaune tsaye suka yi ba daga gwamnatin Indiya ba ne.

Su ma manyan ƴan jam'iyyar BJP da sauran jakadun ƙasashe sun yi tur da kalaman.

Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai mai mambobi 57 OIC, da kuma Pakistan su ma sun soki Indiya.

Masu sharhi sun ce ya kamata shugaban jam'iyyar na ƙasa gaba ɗaya da kuma gwamnatin ƙasar daga ƙololuwa su fitar da sanarwar yin tur da lamarin.

Rashin yin hakan a cewarsu, zai lalata dangantakar Indiya da ƙasashen Larabawa da kuma Iran.

Abin da hakan zai jawo

Indiya da ƙasashen yankin Gulf da suka hada da Kuwait da Qatar da Saudiyya da Bahrain da Oman da kuma UAE, suna kasuwancin da ya kai na dala biliyan 87 daga shekarar 2020 zuwa 2021.

Miliyoyin Indiyawa ne ke zaune suke kuma aiki a wadannan ƙasashen, suke kuma tura miliyoyin daloli zuwa ƙasarsu ga iyalansu.

Yankin shi ne kuma wanda Indiya ta fi shigar da makamashi ƙasarta daga cikinsa.

Firaministan Indiya Narendra Modi yana yawan kai ziyara yankin tun bayan ɗarewarsa mulki a 2014.

Tuni ƙasar ta ƙulla yarjejeniyar kasuwanci marar haraji tsakaninta da UAE sannan tana tattaunawa da sauran ƙasashen don faɗaɗa yarjejeniyar.

Sannan akwai lokacin da Mista Modi ya halarci bikin buɗe wani wajen bauatr ƴan addinin Hindu a Abu Dhabi a 2018 - wanda aka bayyana a matsayin misali na ƙarfafar alaƙar Indiya da yankin Larabawa.

A yayin da dangantaka tsakanin Indiya da Iran kuwa ke sirewa cikin shekarun nan, wannan sabon ce-ce-ku-cen ka iya shafar ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ke shirin kai wa Indiya.

Ƙwararru sun ce ce-ce-ku-cen ka iya shafar nasarorin da Indiya ta yi a baya-bayan nan.

Wasu masu sharhin kuwa cewa suka yi lalacewar dangantakar diflomasiyya tsakanin Indiya da ƙasashen ka iya shafar burikanta.

Ƙasashen Larabawa na ƙoƙarin kwantar da hankulan al'ummarsu

Su ma ƙasashen Larabawa a nasu ɓangaren, suna ɗaukar matakai don kwantar da hankulan al'ummominsu.

An yi ta amfani da maudu'ai na sukar Indiya a kafafen sada zumunta da suka dinga tashe a ƙasashen, kuma lamarin ya zama wanda ya mamaye kanun labaransu.

Wasu maudu'an na kira ne da ƙauracewa kayayyakin Indiya. Sannan rahotanni sun ce wasu kantunan a Qatar da Kuwait sun yi ta cire kayayyakin Indiya daga cikinsu.

Ƙaruwar rabuwar kawuna

Masu suka sun ce ana samun ƙaruwar rarrabuwar kawuna a Indiya tun bayan da BJP ta hau mulki.

Sannan an samu ƙaruwar tashe-tashen hankula a makonnin da suka gabata bayan da wasu mabiya Hindu suka je wata kotu a Varanasi son neman izinin yin ibada a wani tsohon masallaci da suka ce an gina shi ne a gurbin wani tsohon wajen ibadaha.

Tasoshin talabijin sun yi muhawara sannan an samu ƙaruwar kalaman ƙiyayya a shafukan sada zumunta ma kan lamarin.

Amma masu sharhi sun cewa fushin da ƙasashen duniya suka yi kan lamarin ya kamata ya zama izinia ga Indiya.