Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda abokai uku suka nutse a ruwa a Ƙaraye a Kano
Ranar Laraba, 18 ga watan Mayun 2022, rana ce da jama'ar garin Bichi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ba za su taɓa mantawa da ita ba, musamman Idris Umar wanda yana tsaye mutum uku daga cikin abokansa suka rasu bayan sun nutse a cikin ruwa a Ƙaraye a lokacin da suka je wanka a Kogi da safe.
Musa Abubakar mai shekara 25 da Isyaku Bashir, mai shekara 23 da kuma Nazifi Ibrahim mai shekara 19, duk sun rasu a lokacin da suka shiga dam don su yi wanka da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Idris ya shaida wa BBC cewa shi da sauran abokansa sun yi tafiya daga Bichi zuwa Ƙaraye a ranar Talata domin zaman Majalisi.
"Wasu mutane ne a Karaye suka neme mu domin zuwa Majalisin kuma ya kamata mu koma Bichi a ranar amma sai suka roƙe mu da mu ƙara wasu sa'o'i, ko da yamma ta yi sai suka ce mu kwana a Karaye, in ji Idris.
"Da safe, sai aka rinƙa jinkiri wurin kawo ruwan wanka sai ɗaya daga cikinmu ya ba mu shawarar mu je kogi mu yi wanka wanda daga nan ne muka soma tafiya.
"Wasu daga cikinmu ba su saki jiki da dam ɗin ba inda suka ce kada mu je saboda wani mummunan abu zai iya faruwa amma sai Musa (yana cikin waɗanda suka rasu) sai cikin wasa ya ce babu abin da zai faru."
Sai Idris ya ci gaba da bayani kan abin da ya faru a lokacin da suka kai dam ɗin da kuma yadda abokansa uku suka rasu cikin mintoci.
"Dam ɗin yana da ɓangarori biyu, akwai babban wurin wanda muka ƙaurace masa sa'annan akwai ƙaramnin wurin wanda can muka je kuma har muka ga ƙananan yara a wurin da ke wanka.
"Isyaku ne ya soma cire kayansa ya tsunduma cikin ruwan sa'annan Nazifi ya bi shi amma huɗu daga cikinmu sai muka lura cewa ba su fito ba, wanda hakan ya sa Musa ya ce bari ya shiga ya ceto su.
"Ko da Musa ya shiga sai muka lura cewa wani mummunan abu ya faru saboda babu wanda ya fito daga cikinsu sai muka soma ihun kiran mutane.
"Amma abin takaicin shi ne ba a kawo ɗauki da wuri ba saboda bayan minti goma da kusan mutum 20 suka shiga nemansu gawarwakinsu kaɗai aka ciro daga dam ɗin."
Idris ya ce shi da sauran abokansa ba su iya ruwa ba shi yasa suka yanke hukuncin cewa ba za su shiga neman abokansu ba.
Mahaifin Musa ya bayyana cewa ba zai manta lokacinsu na ƙarshe tare da ɗansa ba kafin suka kama hanyar zuwa Karaye.
"Ina kwance a ɗaki a lokacoin da Musa ya shigo ya gaishe ni ɗauke da jaka inda ya ce mani Baba za mu tafi Karaye domin yabon Annabi ni kuma sai na yi masa addu'ar Allah ya tsare su."
Mahaifin ya bayyana cewa ba iyalansa kaɗai za su yi kewar Musa ba, a faɗin Bichi ana amfana da shi sakamakon yana da shaguna biyu na POS wanda yake taimakawa domin cire kuɗi.
Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana reshen Jihar Kano Saminu Yusuf ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce ba a tuntuɓe su ba wurin neman ɗauki kuma a lokacin da suka isa wurin masu iyo a cikin ruwa tuni suka ciro gawarwakinsu daga dam ɗin.
Ya bayar da shawara ga musamman baƙi da su guji shiga ruwan da ba su saba da shi ba.
Wani bala'i da kuma ya faru a Bichi
Watanni biyu da suka wuce, zaftarewar ƙasa ta kashe mutum huɗu a ƙauyen Yanlami wanda ke ƙarƙashi Karamar Hukumar Bichi a lokacin da mutanen suka haɗa hannu domin gina gida ga wani abokinsu wanda yake so ya yi aure.
Ya rage kimanin wata guda ga Musa Jibril mai shekara 25 ya auri Rabi Tofawa, kuma kamar yadda ake yi a al'adance a ƙasar Hausa, abokansa sun haɗu domin taya sa gina gidan ƙasa wanda a nan ne shi da matarsa za su zauna bayan aure.
Hashim Yunusa aboki ne ga Jibril kuma yana daga cikin mutum biyu waɗanda shaidun gani da ido ne waɗanda suka ga yadda komai ya faru.
"Yadda abin yake shi ne su biyar za su shiga cikin rami suna miƙo ƙasa ni kuma da Sani za mu tsaya a waje muna karɓar ƙasar muna sakawa a amalanke domin kaiwa wurin ginin.
"Mun riga mun kai sahun farko na ƙasar kuma kafin mu tafi har muna wasa da juna inda muna kan hanyar komawa a sahu na biyu sai muka hangi ƙura mai ƙarfi inda muka yi sauri muka je wurin muka iske ƙasa ta binne su.
"Hakan ya sa muka yi sauri muka shiga cikin ƙauye muka kira jama'a kuma kafin mu sani tuni jama'a suka cika wurin kuma har daga ƙauyukan da ke kusa mutane sun zo don su taimaka amma zuwa lokacin da suka zo suka ciro gawarwakinsu duk sun mutu."
Wasu lokutan da aka samu labaran nutsewa da ya ja hankalin jama'a a a Najeriya
A 2017, gwamnatin Najeriya ta yi jaje ga iyalan ɗaliban da suka rasu a lokacin da suka yi tafiya daga makarantarsu zuwa Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Ɗaliban sun kai ziyara ne a wani wurin aikin ruwa inda aka samu hatsari kuma da dama daga cikinsu suka rasu.
Haka ma 2021 mutane da dama sun rasu bayan kwale-kwale ya kife a kogin Bagwai da ke Jihar Kano.
Hukumomi sun bayyana cewa sun ceto mutum bakwai da kuma ciro gawarwaki 29.
Waɗanda suka shaida lamarin sun ce kwale-kwalen ya nutse ne sakamakon tsananin lodi da aka yi masa.
Haka kuma dai a 2021 jama'a da dama ne suka rasu a cikin wani kwale-kwale da ya nutse a Jihar Kebbi a yayin da fasinjojin kwale-kwalen waɗanda akasarinsu mata ne da yara suka baro Jihar Neja inda kwale-kwalen ya nutse.