Burkina Faso: Matan masu haƙar ma'adinan da suka rufta tsawon wata ɗaya na cikin fargaba

- Marubuci, Daga Lalla Sy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Réo
- An wallafa
A kowacce rana, tashin muryoyin mabiya addinin kirista ke tashi su na addu'a ga 'yan uwansu da suka maƘale a mahaƘar ma'adinin zinc su fito lafiya wata daya da ya wuce a Burkina Faso, ba su karaya ba kullum suna fatan ganin 'yan uwansu.
Kwanaki 31 masu aikin ceto suka yi kafin isa wurin ceto na farko da ake kyautata zaton masu hakar ma'adinin sun fake, lokacin da ambaliyar ruwa ta fadawa wurin hakar mallakin 'yan Canada, bayan mamakon ruwan da aka fuskanta a ranar 16 ga watan Afirilu.
Amma a lokacin da aka bude wurin a farkon wannan makon, babu ko daya daga cikin mutanen da aka gani, da suka hada da 'yan kasar 6, da dan Zambia sai kuma dan Tanzania.
A yanzu iyalai da 'yan uwansu, na fatan idan aka bude mafaka ta biyu wadda ke karshen mahakar ma'adinan mai zurfin mita 710 za a gan su.
Mafakar da ake kira dakin kubuta, an rufe ta ta sama, sannan an tanadi iskar Oxygen da za su shaka cikin sauki da ruwan sha da dan abin taba ka lashe.

'Yan uwan mutanen da suka kai mata 20, sun yi zaman dirshan a wani budadden fili da ke Reo nisan mil bakwai daga wurin hakar ma'adinan.
Wasu zaune kan tabarmi wasu kujerun katako dauke kuros a hannu-su na ta addu'o'i.
Hukumomi sun isa wurin a ranar Talata, domin sanar da su bakin labarin ba ga 'yan uwansu a mafaka ta farko da aka bude ba mai nisan mita 560 a kasa.
An bukaci 'yan jarida su bar wajen, domin barin iyalai su ji da lalurar da ta same su, wani malamin addinin musulunci ya bi tawagar jami'an inda ya gabatar da addu'a da karfafawa iyalan gwiwa.
Amma hakan bai hana jin shesshekar kuka da nannauyar ajiyar zuciya ba, wata mace cikin tashin hankali da kaduwa ce ke kuka cikin gunji tamkar za ta amayar da 'yan cikinta.
'Ba za mu karaya ba'
Sai dai Edith Moné, matar daya daga cikin masu hakar, ta shaida min ita da sauran matan ba za su bar wurin ba, da suke karfafawa juna gwiwa har sai abin da hali ya yi.
"Idan na je gida na ga 'ya'yana, sai na tuna yadda suke tarbar babansu idan ya dawo daga aiki, ina tuna yadda ya ke wasa da su. Ina fargabar komawa gida, ba zan iya jurewa ba.
Ta yi zuru-zuru, idanunta sun koɗe saboda tsananin kuka: "Za mu zauna anan har sai mazajenmu sun fito daga wannan ramin."

Har yanzu ta na fatan mijinta zai fito a raye, sai dai ta amince dole ta karbi duk kaddarar da ta zo mata: "Idan mazajenmu sun mutu, ba mu da zabi face yin juriya da karbar ƙaddararmu."
Aisha Kinda, wadda ke da ciki, ta shaida min tun ranar 5 ga wata matan suka zo wajen da niyyar yin zanga-zanga a kuma ba su bayanai kan mazajensu.
Ta ce addu'a suke yi Allah ya yi ikonsa: "Ina matukar bukatar shi a rayuwarmu. Ina tsananin kewarsa, yana kyautata min da sanya ni farin ciki."
Kwararru daga sassa daban-daban na duniya
An dakatar da dukkan ayyuka a wurin, wanda ke nisan kilomita 120 daga babban birnin kasar, Ouagadougou, an mayar da hankali kan aikin ceto mutanen.
Hanyar zuwa mahakar ma'adinan mai cike da duwatsu, dai ta kasance wadda ababen hawa da ma'ikata ke zuruftu.
A yanzu dai, aikin ceton kadai ake yi a ramin mai cike da duhu.
Sama da wata guda kenan da lamarin ya afku, aikin ceto cikin sa'a 24 na tafe, ta hanyar amfani da kayan aiki na musamman da za a kawo daga kasar Ghana da Afirka ta Kudu.
An zuba miliyoyin litar ruwa cikin mahakar ma'adinan, domin samun damar isa ga mutanen da watakil su na mafaka ta farko.
Bayan mahaukacin ruwan da aka sheka cikin ramin, ruwan ya kwanta a kasa nisan mita 520.
Yanayin da injiniyoyin ke aiki na kokarin isa inda abokan aikinsu suka makale, su na aiki cikin tsananin zafi da fargabar halin da suke ciki.

Asalin hoton, Reuters
Yayin da ake fatan masu aikin ceton za su kubutar da su ta hanyar mayar da hankali a mafakar, ana fargabar babu wani alamu da suka nuna mutanen suna wajen.
Matar daya daga cikin mazan ta shaida wa BBC cewa, mijinta yana aiki ne a zurfin mita 6210 ko 620 a can kasa a lokacin da ruwa ya shiga ramin: cikin kasa da awa daya an tafka ruwan da ya kai mita 125, wato ya rubanya sau biya idan aka kwatanta da ruwan saman da ake yi na ko da yaushea watan Afirilu.
"Mun kawo kwararru daga sassa daban-daban na duniya. Muna da kwararru daga kasashen Australia da Afirka ta Kudu da kuma Canada," in ji Ricus Grimbeek, shugaban kamfanin Trevali Mines Corporation, kuma shi ne mamallakin wurin hakar ma'adinai Perkoa.
Sai dai ya amince yanayin da ake aikin na nufin akwai matukar wuya da karya gwiwa.
"Ya kamata mu fuskanci gaskiya, wurin fakewar da ke cikin ramin gakiya ba wuri ne da zai iya rike ruwa da yawa ba. An yi shi ne domin duwatsu da da iskar gas su fice."

A ranar Talata, kamfanin ya ce ma'aikatan ceto na ci gaba da aiki babu kakkuatawa dare da rana domin ganin an samu wani abu, ba kuma za su dakata ba sai an gano mutanen.
"Wannan labari ne mai ta da hankali, mu na amfani da wannan damar domin mik sakon jaje da tausayawa ga abokan aikinmu, da iyalai da 'yan uwan da abokan arzikin wadanda lamarin nan ya shafa, hakika lokaci ne na bakin ciki da tashin hankali," cewar Mr Grimbeek.
Ministan ma'adinan Burkina Faso, Jean Alphonse Somé, ya tabbatar aikin ceton ya yi matukar nisa.
"Gwamnati na aiki tukuru za kuma ta ci gaba da da aikin tunra wuta can karkashin ramin hakao ma'adinan, domin gano ko 'yan uwanmu takwas sun samu isa dayar mafakar da muke kyautata zaton sun samu isa cikinta," in ji Mr Somé.
Kamar yadda masu sa ido suka bayyana, dukkan jami'ai daga na gwamnati har da na mahakar ma'adinan, sun san yadda wurin ya ke da matukar hadari da yanayin aikin na rashin tabbas.
Ga shugabannin addinai a wannan yanki na Burkina Faso, sun san tabbas ba lallai a fito da su duka a raye ba, dole akwai wadanda za su binne.
Yayin da wasu suka yanke hukuncin ba lallai mutanen su kasance a raye ba, a bangare guda kuma babu wanda zai bada kai ko karaya har sai sun ga an fito da gawar mazajen, kafin za su hakura su rungumi kaddara.











