Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ukraine: Wani sansanin yara da ya zama wurin kashe mutane a Rasha
- Marubuci, Daga Sarah Rainsford
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eastern Europe correspondent, Bucha
- An wallafa
Tun bayan fatattakar sojin Rasha daga Kyiv a karshen watan Maris, an gano gawawwakin farar hula 1,000 a yankin Bucha, yawanci an binne su a manyan kaburbura.
BBC ta gano kusan mutum 650 an harbe su ne da bindiga, a wani mataki da babban jami'in 'yan sanda ya bayyana da kisan gilla.
Sarah Rainsford ta yi bincike kan abin da ya faru da yara kanana da ke sansanin, wanda a yanzu ake gani da wurin da aka aikata muggan laifuka.
*Muna gargadin wannan rahoto na dauke da bayanan da ka iya dagawa wasu hankali*
Abu ne mai sauki ka gagara gane inda aka aikata kisan ta farat daya.
Amma a gidan karkashin kasa mai damshi da aka tara shirgi, da katako da akai amfani da shi a matsayin mashigar Bucha gabannin yakin, an tilastawa wasu maza biyar 'yan Ukraine durkusawa kan gwiwarsu, ka na aka sakar musu dalma a goshi.
A kofar shiga wurin, akwai duwatsu malale da jini, da ya sauya launi zuwa baki saboda bushewa.
A gefen nan kuma wata hanya ce siririya, da wani karfe da shi ma tamkar an shafe ta da jini.
A jikin bangon kuma, huda ta kai 12 da suka faru sanadiyar harbin bindiga.
Dan taki kadan daga wurin da sauran tarkacen kayan sojin Rasha, akwai wata kwatanniya dauke da dafaffiyar shinkafa da nama, sai kuma wani kwalin biskit da aka cinye.
An yi rubutu da zane baro-baro na rakumin dawa da ke nuna karara wannan sansanin yara ne.
Amma a lokacin da sojojin Rasha suka kutsa Bucha, da ke wajen birnin Kyiv, a farkon watan Maris, wannan sansani ya zama tamkar mayankar mutane.
Labarin kisan da aka yi a sansanin yaran mai tada hankalin, haka nan bayanan da za mu kawo muku nan gaba ba masu dadi ba.
An kashe sama da farar hula 1,000 a yankin Bucha, lokacin da sojojin Rasha suka mamaye shi na wata guda, sai dai yawanci ba wai harin bama-bamai da na atilari ne ya kashe su ba.
Sama da mutum 650 sojojin Rasha ne suka bindigesu, kamar yadda wani babban jami'in 'yan sanda ya bayyana.
A yanzu Ukraine ta fara farautar wadanda suka kashe su.
Volodymyr Boichenko mazaunin Hostomel ne, da ke tsallaken Bucha, kusa da wani katon sarari da jiragen sama ke sauka, anan ne kuma wuri na farko da sojojin Rasha suka fara sauka domin kokarin hambarar da gwamnatin Ukraine.
A lokacin da 'yar uwarsa Aliona Mykytiuk ta yanke shawarar tserewa daga yankin kafin yakin ya cimmata, ta yi ta rokon Volodymyr ya zo su tafi tare.
Farar hula ne shi ba soja ba ne amma ya kafe kan ya na son tsayawa domin taimako.
Ya kwashe kwanaki ya na neman abinci da ruwa a Hostomel domin taimakawa makofta ciki har da yara kanana da suka makale a wuraren karkashin kasa saboda firgicin barin wuta da makaman roka da Rasha ke yi.
Mai shekaru 34 da ya zagaya duniya a jiragen ruwan sojoji, ya na da faran-faran, a kullum sai ya kira iyayensa domin tabbatar mu su da lafiyarshi.
Aliona kan kagu da jiran kiran wayarsa, ta san dole sai ya tafi kan tudu sannan ya ke samun sabis din waya, idan kuma aka samu matsalar ruwan bama-bamai to sai ya yi da gaske kafin ya kubuta.
A daidai lokacin da kayan abinci suka fara yankewa, ta bai wa dan uwanta ya tsere daga Bucha, a lokacin tuni an rufe hanyoyi.
A ranar 8 ga watan Maris ta karshe da Aliona ta ji mutuwar Dan Uwanta ita ce ranar 8 ga watan Maris. Volodymyr ba ya daga cikin mutanen da ke nuna damuwa.
Amma a wannna ranar ya Shaida mata Kar ta damu da shi.
Ya ce min ''ina matukar son ki" na ji bacin ran fadar haka," Aliona ta fashe da kuka, ya na murje idanunta Amma ta kasa tsaida hawayen.
"Akwai alamun tsoro a muryarsa" kwanaki hudu bayan nan, makofta suka ga Volodymyr a kusa da Promenystyi, fitaccen wuri da aka sani da sansani, daga nan ba a kara ganin shi ba.A watan Maris, fada a Kyiv ya kara munana, ɗan karamin birnin Bucha ya Zamo sansanin Yaki. Kanyewar dakarun Rasha a farkon watan Afirilu, ya bayyana abin da ya firgita duniya da: gawawwakin mazauna Bucha yashe akan tituna, a Inda aka harbe su.
Tasha ta shaidawa masu sauraronta an kitsa kashe-kashen ne, wani lamari da kowa ya san karya ce. A kokarin Ukraine na hukunta wadanda suka aikata kisan, da bincike da tattara shaidu a yankunan da a baya Rasha ta kwace yanzu sun dawo hannunta. "Ba mu san shirin Putin haka ya ke ba, mu na aiki cikin gaggawa domin tattara shaidu, domin kaucewa jefa mana bama-bamai domin batar da shaidar da muke da ita," in ji shugaban ƴan sandan birnin Kyiv wato Andrii Niebytov. Shaidun sun hada da wani fili cike da motocin farar hula da aka yi mu su barin albarusai, a yanzu an tara su a wajen Bucha.
Motocin da akai wa barin wuta me loakcin da iyalai ke kokarin tserewa daga yankin.
Daya daga ciki na dauke da farin kyalle a jikin taga, alamun sojojin da ke cikin motar ba wata barazana ce ba. Da zarar ka matsa kadan babu abin da za ka ji sai warin gawa.
A lokacin da aka gano gawawwakin da ke sansanin Radiant a ranar 4 ga watan Afirilu, Volodymyr Boichenkon na daga cikin mamatan.
Aliona ta dauki watanni ta na kiran asibitoci da wuraren ajiye gawa daban-daban.
A wannan ranar aka tura mata hoto domin tantance gawar. Ta san cewa Dan uwanta ne tun ma kafin ta bude hoton.
"Na tsane su, tsana ta har abada," in ji Aliona cikin kuka, kan wadanda suka kashe mata Dan'uwa.
"Na san bai dace na fadi haka ba a kan mutane, Amma ba bil adama ba, babu wani sashe na jikinsu da ba a azabtar ba ta hanyar duka."
An gano gawar mazan biyar, durkushe akan gwiwarsu, an daure kawunansu ta baya. "Mun san an azabtar da su" shugaban'yan sandan ya shaida wa BBC.
"Sojojin Rasha sun wuce makadi da rawa, da dokokin yadda ake yin yaki. Ba da sojoji suke Yaki a Ukraine ba, su Na sacewa da azabtar da farar hula da ba su san hawa bare sauka ba."Sai dai masu shigar da kara, da ofishin jami'in tsaro ba su yi karin haske kan bincike da ake yi, wasu daga cikin sojojin Rasha sun yi sake wajen rashin boye shaidun da za a iya gane su da gaggawa.
Jami'an da ke kare iyakokin Ukraine sun bayyana jerin sunayen sojojin Rasha a wasu daga cikin wuraren da aka watsar.
Daya daga ciki ya nuna aikin musaya suke yi ba aikin, wani daga ciki ma na dauke da bayanan fasfo din wani har da lambar waya..
Aiki ne mai dinbin yawa, amma duk da haka an yi rijistar mamata 1,00, ya yin da jami'an tsaron Ukraine sun yi kira a kara amfani da fasaha wajen nemo karin farar hula da ke bukatar taimako.
"Ina jin cewa wannan lokacin aiki ne," in ji Dmytro Replianchuk, dan jarida da ke aiki da tashar lidstvo.info, wanda ya ke binciken bankado danbarwar cin hanci da rashawa da take doka da oda da ake yi wa jami'an tsaron Ukraine gabannin fara yakin.
A yanzu ya na cikin tawagar masu shigar da kara, domin samar da bayanan intanet da za su taimakawa a kamo wadanda akje zargi da aikata laifukan yaki.
"Abu ne mai matukar wuya, hanyoyi da dama ba za su yi aiki ba. Amma duk da hakan a 'yan makwannin nan, ya na da matukar muhimmanci a samu bayanan da suka dace in ji Dmytro.
Mun gano wani abu mai muhimmanci a kusa da sansanin Radiant, wani kunshin sako da wata mace mai suna Ksyukha ta aikawa iyalan wani sojin Rasha wanda aka rubuta sunansa da mukami baro-baro a jiki. Runduna ta 6720 da ke Rubtsovsk, da ke yankin Altai a Siberia.
A baya wurin na da alaka da Bucha, kafin a na'urar CCTV ta gano sojojin Rasha su na aikawa 'yan uwansu kunshin kayayyakin da suka sace a gidajen 'yan Ukraine.
Ba za mu iya tabbatar da ko sojojin Rubtsovsk sun zauna a sansanin yaran ba, ko kuma su na wajen a lokacin da aka kashe mazan.
Da fari 'yan sandan na bukatar samar da kwararan shaidu kan kisan.
"Mu na aiki kan hakan, sai dai aikin na tafiyar hawainiya," in ji Mr Niebytov. "Sansanin dai shalkwata ce, dan haka dole akwai kwamandan da ke kula da shi.
Sojojin ba za su kashe kowa ba tare da sanin kwamandan su ba. Don haka za mu fara neman wadanda suka shirya kisan da wadanda suka aiwatar da shi."
A tsallaken titin da sansanin Radiant ya ke, a bayan wata majami'a da aka lalata, mun fara ganin alamun da ke nuna akwai rayayyu a wajen.
Yara ne kanana suke wasa a bayan wani gida, ya yin da wani mutum ke dauke da fallen katako ya na kokarin sanyawa a tagogin gidan.
An kuma bude wani dan karamin shago domin saida 'yan kayan masarufi da mutanen da suka fara komawa za su yi amfani da su.
A garuruwan da ke makoftaka, su na bayani kan ranar da tankokin yakin Rasha suka shiga garin, sojojin na yin harbin kan mai uwa da wabi musamman idan sun yi markas da barasa, suna fasa gidajen mutane tare da sace kayansu.
Sun tuna wani mutumin garin da ya kubuta ya tsallako daga sansanin Radiant, sun ba shi mafaka duk da hadarin hakan.
Viktor Sytnytskyi bai san sansanin Radiant ba, amma dukkan bayanan da ya ba da sun yi daidai da wanda muka samu.
A yanzu ya na yammacin Ukraine, ya shaida min labarin halin da ya shiga ta wayar tarho, mun yi hirar a lokacin ya na zaune a mota, baya son mahaifiyarsa ta ji wannan tashin hankali.
A farkon watan Maris ne sojojin Rasha suka sace Viktor akan titi. Sun daure masa hannu, tare da rufe masa fuska da hular shi, daga nan suka hankada shi wani wuri da ya tabbatar gidan karkashin kasa ne kuma sansanin yara.
Anan wurin, sojojin Rasha suka shekawa kafafunsa ruwa mai sanyi, domin ya sandare sun kuma dora bakin bindiga a kansa.
"Sun yi ta nanata, 'Ina 'yan siyasarku? Ina sojojin? Ina Zelensky ya ke? Viktor ya tuna daya daga cikinsu ya ambaci sunan Putin sai na fadi kalma maras dadi akan shi, ai kuwa na sha dukan kawo wuka".
Ya tuna fusatar da ya yi da sojin da suka kama shi, da abubuwan ban tsoro da takaicin da suka faru a lokacin.
A baya ya yi aiki a birnin Moscow da wasu mutanen Siberia, ya kada matuka da ya yadda sojojin Rasha ke azabtar da shi. Har a kwai lokacin da wani soja ya bayyana masa shi ma dan Siberia ne.
Viktor ya shaida masa ya na bakin cikin yadda lamura suka lalace haka.
"Abin takaicin shi ne kakannin mu sun hada karfi da karfe domin yakar 'yan Nazi, amma yanzu kai ma ka shigo cikinsu," wannan ce amsar da sojan Rashar ya fada cikin fusata.
"Ya shaida min: 'Ka ma tuna duk abin da za ka tuna kan abin da ka gani, idan ba haka ba, watakil harbe ka za a yi.'"
Allah ya bai wa Viktor sa'a a wannan daren. An yi ruwan bama-bamai, da ya lura sojojin da suka sace shi ba sa gadin shi, sai ya yi amfani da damar ya tsere.
"Na yi lissafin ba ni da wata dama ta kubuta in ba wannan ba, kuma gara bama-bamai su kashe ni da na zauna a kashe ni a karkashin kasa.
"Abin da za su yi dai bai wuce su harbe mi ba, mutuwa daya ce?"
Akwai tarin kaburbura a karkashin sansanin yaran, a yanzu an yi jana'izar Volodymyr Boichenko wanda aka binne karkashin bishiyar furen blossom da ke tsohuwar makabartar Bucha.
Bayan an binne shi, Aliona ta ce a karshe ta ga fuskar dan uwanta a mafarki, tamkar ya na lallashin ta.
Amma har yanzu ta na da tarin tambayoyin da babu amsoshinsu. Kuros din da aka sanya a kan kabarin Volodymyr abin tunawa da ranar haihuwarsa, ba wai tunawa da ranar mutuwarsa ba, saboda 'yan uwansa ba su san ainahin ranar da aka kashe shi ba.
Ba lallai su sa ni ba, sai idan an gano kwamandan sojin Rasha da ya jagoranci sojin a sansanin Radiant inda aka samu gawawwakin.
Kamar sauran mutanen Bucha, duk da sun san farar hula ba wai yaki ne kadai ya rutsa da su kadai ba.
A'a dama canan yi niyyar aikata hakan gare su, ko dai sojojin Rasha ba su san dokokin yaki ba, ko kuma sun sani sun aikata abin da ran su ya raya musu.
Dukkan hotunan na da hakkin mallaka
Wadanda suka taimaka wajen samun bayanan: Daria Sipigina, Mariana Matveichuk da kuma Tony Brown