Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ukraine: Hanyoyi biyar da za su kawo karshen yakin Ukraine da Rasha
- Marubuci, Daga James Landale
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan harkokin difilomasiyya
- An wallafa
Hazon yaki ba zai bari a ga abin da ke tahowa ba.
Labaran yakin da ake gwabzawa da kai komon diflomasiyya da tashin hankalin wadanda suka yi rashi: dukka wadannan abubuwan na iya buwayar mutane.
Saboda haka ne za mu sarara domin duba yadda rikicin Ukraine zai iya kasance a karshe.
Wace irin makoma 'yan siyasa da masu tsare-tsaren yaki ke tunanin za a samu bayan rikicin ya zo karshe? Mutane kalilan ne za su iya yin hasashen abin da zai iya faruwa. Yawancin abubuwan ba masu karfafa gwuiwa ne ba.
Gajeren yaki
A karkashin wannan tunanin, Rasha za ta bude wuta sosai. Za ta rika kai hare-hare na mai uwa da wabi da makaman atilari da na roka a Ukraine.
Sojojin sama na Rasha - wadanda kawo yanzu ba su taka wata rawar gani ba - za ta fara ragargazar Ukraine.
Za kaddamar da hare-hare ta intanet, wadanda za su gurgunta na'urori da ma'aikatun da suka dogara da intanet wajen gudanar da ayyukansu.
Za a dakile hanyoyin samar da makamashi da na sadarwa. Dubbna 'yan kasar za su rasa rayukansu.
Jajircewan da sojojin Ukraine ke yi bai hana kasar komawa hannun Rasha ba cikin kwanaki.
Za a mye gurbin gwmnatin da wadda ke yi wa Rasha biyayya. Za a kashe Shugaba Zelensky ko kuma zai tsere zuwa yammacin Ukraine ko ma zuwa kasashen waje.
Ukraine za ta bi sahun Belarus a matsayin kasashen da ke karkashin kulawar Rasha.
Makoma irin wannan mai yiwuwa ce amma za ta dogara ga sauyawar abubuwa masu dama:
Na farko a ce dakarun Rasha sun kara kaimi sosai, da kara yawan dakarun na Rasha. Mista Putin na iya sauya shugabannin kasar a Kyiv wanda zai kawo karshen yunkurin shigar da Ukraine Tarayyar Turai.
Amma dukkan wata gwamnati da Rasha za ta kafa za ta kasance haramtacciya a idon duniya. Irin wannan makomar za ta zama mai wuyar dorewa.
Dogon yaki
Abin da ya fi zama mai yiwuwa shi ne wannan yakin na iya zama rikicin da za a shafe shekaru ana yinsa.
Watakila Rasha za ta makale a cikin kasar saboda rashin iya gudanar da yakin.
Watakila dakarun Rasha za su bata lokaci kafin su iya mallakan birane kamar Kyiv wadanda masu kare biranen ke yakar Rashawa daga layi zuwa layi.
Za a iya cewa za a dade ana rikicin, kuma yana tunatarwa da yakin da Rasha ta yi a babban birnin Checheniya wato Grozny a shekarun 1990.
Yakin nahiyar Turai
Shin yana yiwuwa wannan yakin ya fita daga iyakokin kasar Ukraine zwa kasashen da ke kusa?
Shugaba Putin na iya fadafa rikicin ta hanyar mamaye tsofaffin jamhuriyoyin tsohuwar tarayyar Soviet kamar Moldova da Georgia da ba su shiga kuniyar tsaro ta Nato ba.
Mista Putin na iya ayyana taimakon makaman da kasashen yammacin Turai ke ba Ukraine a matsayin takalar fada wanda ke bukatar ya mayar da martani.
Yana kuma iya tura sojinsa zuwa kasashen yankin Baltic da ke cikin kungiyar Nato - irinsu Lithuania domin ya samar wa kasarsa ata mashiga ta doron kasa zuwa wani yankin Rasha mai suna Kaliningrad.
Yaki da Nato zai kasance mai matukar hatsari.
A karkashin Sashe na 5 na doar da ta kafa kungiyar tsaron idan aka kai wa wata kasa daya da ke mamba ce ta kungiyar, sauran kasashen za su dauka an kai wa dukkansu harin ne.
Hanyar Diflomasiyya
Shin, akwai wata hanyar diflomasiyya da za a iya bi duk da rincabewar da al'amura suka yi?
Lallai har yanzu ana tattaunawa da juna.
Shugaba Macron na Faransa ya yi magana da Shugaba Putin ta wayar tarho. jami'an diflomasiyya sun ce har yanzu ana laluben hanyoyin sasanci da rasha.
Kuma wani abin mamakin shi ne jami'an gwamnatin Rasha da na Ukraine na ganawa da juna a kan iyakar Ukraine da Belarus. Da alama Putin bai kulle kofar yin sasanci ba kan wannan batun.
Tambaya a nan ita ce: Shin kasashen yammacin Turai na iya yi wa Rasha tayin wata hanyar janyewa daga rikicin ba tare da ta ji kunya ba?
A hambarar da Putin
To ya batun makomar shi kansa Shugaba Putin? Yayin da ya tura sojojinsa su mamaye Ukraine,ya ce: "Mun shirya wa dukkan sakamako."
Amma mai zai faru idan sakamakon shi ne a hambare shi daga mulki? Wasu na iya cewa ba abu ne mai yiwuwa ba.
Amma duniya ta sauya cikin 'yan shekarun nan, ta yadda a na ganin yiwuwar haka.
Farfesa Sir lawrence freedman na Jami'ar nazarin dabarun yaki ta Kings College, da ke birnin Landan ya rubuta wadannan kalaman cikin wannnan makon:
"Akwai yiwuwar za a iya samun sauyin gwamnati a Moscow kamar yadda za a iya samun sauyin gwamnati a birnin Kyiv.
Mene ne zai wakana a karshe?
Wadannan abubuwan na iya faruwa a kadaice, ko tare - kuma wasunsu na iya aukuwa tare su kuma haifar da wani sakamakon na daban.
Sai dai ko ya wannan rikicin ya ya kaya, sauyi ya zo a duniya. Ba za ta sake komawa gidan jiya ba.
Dangantakar Rasha da sauran kasashen yammacin Turai ta sauya ke nan, kuma yadda Turai ke kallon siyasar yankin zai sauya na dindindin.