Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matan da suka zabi haihuwa ba tare da maza ba a fadin duniya
- Marubuci, Daga Sandrine Lungumbu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Sama da kashi 50 cikin dari na mata da ke amfani da maniyyin da ake bayarwa kyauta wanda ake sa musu a mahaifa su haihu, mata ne da ba su da maza, wadanda suka kuduri aniyar renon 'ya'yansu har su girma su kadai ba tare da wani namiji ba, kamar yadda bayanai na baya-bayan nan daga daya daga cikin manya-manyan cibiyoyi na duniya masu adana maniyyi, Cryos International suka nuna.
Bayanan daga Cryos wadda ke samar da daskararren maniyyi da aka adana da kuma kwai (maniyyin mata) ga kasashe sama da 100 a duniya sun nuna karuwar yawan mata marassa maza da ke karbar maniyyin a cikin shekara bakwai da ta wuce, inda yawan ya tashi sama sosai zuwa kashi 54 cikin dari a 2020
A fadin duniya akwai sama da mata miliyan 100 da ba su da maza wadanda ke kula da 'ya'yansu har su girma ba tare da tallafin wani namiji ba, kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta nuna according to UN Women.
Kodayake babu wasu cikakkun bayanai a kan yawan matan da ba su da maza bisa radin kansu da kansu, matan da suka zabi su haihu sannan su kula da 'ya'yansu har 'ya'yan su girma sukan fuskanci tsangwama da ma kalubale na shari'a da zarar sun fara tara 'ya'ya bisa tsari na kansu.
Mun tattauna da wasu mata hudu a kan yadda rayuwarsu ta kasance daga lokacin samun ciki da kuma kula da 'ya'yan har su girma ba tare da namiji ba
'Shawara ce mafi kyau a rayuwata'
Mam Issabre daga Faransa, ita burinta ne a rayuwa ta haihu, kuma bayan shekaru tana tunani kan lamarin a karshe shekara biyu da ta gabata ta yanke shawarar samun cikin ba tare da namiji ba, kuma bayan ta haihu ta kula da dan ita kadai.
Ta ce: "Na yanke shawarar na tattauna batun da mahaifiyata, inda ta ce min kina iya gwadawa ko za a dace, wanda a lokacin ina shekara 38.
"Na tsayar da shawara a Disamba kuma zuwa Fabrairu na samu ciki,'' in ji ma'aikaciyar rediyon.
Bayan wata tara, Mam ta haifi 'yarta mace wadda ta sanya wa suna Imany
Abin kamar ba wuya a baki, to amma da farko sai da ta yi fama da dabaibayin dokoki domin a lokacin ba a bai wa matar da ba ta da miji ko ba ta tare da wani namiji kulawar da ta shafi haihuwa a Faransa a lokacin.
Likitanta ya ba ta shawara da ta je wata kasar inda za a iya dasa mata maniyyi a mahaifarta, to amma sai ta yi sa'a ta samu wani likitan da zai iya yi mata aikin.
'Kyauta daga Allah'
Shekara ɗaya bayan haka, Mam na fatan zama uwa.
"Lokaci na farko da na riƙe 'yata a hannuna lokacin ne na tabbatar da cewa ni uwa ce," a cewarta. "Na sha kuka sosai a ranar nan."
"Wani lokaci mai cike da shauƙi - ita ce shawara mafi kyau da yanke a rayuwata," in ji ta.
Mam ta yanke shawarar neman mutum a ɓoye wanda ba zai bayyana sunansa ba saboda tana so ta kare 'yarta.
A cewarta: "Ba na son ta ji cewa kamaar tana da uba alhalin shi kuma yana ganin mai taimako ne shi kawai.
"Ina fatan wannan ya zama shawara mafi kyau gare ni da kuma 'yata, amma zan yi mata bayanin komai idan ta girma.
"Fatana shi ne na samu 'ya'ya huɗu ko biyar, amma kuma ina ƙara tsufa. To ko ɗa ɗaya na samu babbar kyauta ce daga Allah."
'Na ji kamar shi ne duniyata, ni ma kamar ni ce tasa'
Anne Marie Vasconcelos, wata mai shekara 44 daga New Jersy a Amurka, zama uwa ba ƙaramin abu ba ne.
Shekara 10 da suka gabata, an gano cewa Anne Marie na ɗauke da cutar polycystic ovary syndrome (PCOS), wadda ke shafar yadda ƙwan haihuwa na mace ke aiki da kuma samun matsala wajen haihuwa.
"Likitana ya ce sakamakon gwajin da aka yi mani zan samu matsala wajen haihuwa amma idan ina son haihuwa zan iya nemanta," a cewar ma'aikaciyar gwamnatin tarayyar.
Sai dai a wajen 'yar shekara 34 ɗin da ba ta da miji, ba ta hango cewa za ta iya zama uwa nan kusa.
"Na faɗa mata cewa ba ni da aure, sai ta amsa cewa ba sai kina da miji ba za ki samu 'ya'ya. Ban taɓa tunanin haka ba," kamar yadda take tunawa.
A matsayina na mai bin ɗariƙar Katolika sau da ƙafa, Anne-Marie ta ce zama uwa ta hanyar dasa mata ƙwai a ciki abu ne da ya saɓa wa al'ada, wanda take son gujewa. Tattaunawa da fasto ɗinta ta taimaka.
"Ya faɗa min cewa idan na bi wannan hanyar, 'ya'yana za su iya ci gaba da bin Kiristanci," a cewarta, saboda haka duk da cewa ba zai goyi bayan dasa ƙwai a mahaifa ba amma ba zai tuhume ni ba ko kuma dangina."
"Sai da aka dasa min ƙwai sau biyar da kuma tiyata biyu kafin na haifi ɗana na farko.
"Na kashe dala 95,000 saboda baya cikin tsarin inshorar lafiya nawa. Saboda haka na ɗebo duk kuɗina da bashin ritaya sannan kuma na sayar da gidana."
'Da ma na sani'
Sarah (ba sunanta na gaskiya ba ne) ta yi ta fatan zama uwa.
"Ba na jin akwai wani lokaci a rayuwata da na yi tunanin zan yi ko ba zan yi ba - da ma can ina sane," a cewar mai shekara 36 ɗin.
A cewarta, annobar korona ce ta sa ta fara tunanin ba zai yiwu ta ci gaba da jira ba.
"Annobar ta ba ni damar son na ji ina son zama uwa, don haka na roƙi wani abokina, ya kuma yarda na ɗauki cikin ɗansa," in jita.
A watan Agusta ne Sarah ta gano cewa tana da cikin bayan gwajin su na farko.
Wata shida da samun cikin ta yi waiwaye kan yadda ƙuruciyarta ya sa ta ɗaukar wannan mataki.
"A Labanon na girma lokacin ana yaƙin basasa. An haife ni a lokacin da ake tsananin yaƙi," in ji ta.
"Na ji dadin ƙuruciyata amma kuma ɗimuwa da tsoro sun dabaibaye ni."
Iyayen sun yi aure tsawon shekara 40, amma Sarah ta ce duk da cewa suna gida ɗaya, to kowa zamansa yake yi tsawon lokaci ba abin da ke haɗa su.
"Ba su dadin zamansu tare ba," in ji ta, "zaman nasu marar daɗi ne sosai kuma hakan ne ya taɓa ni har ya sa ni ɗaukar wannan matakin."