Labaran tsofaffin da suka koma makaranta don yin digiri

    • Marubuci, Daga Saroj Pathirana
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Idan ka yi tunanin jam'ia, abin da za ka rinƙa tunani a kanka shi ne ɗan shekara ashirin da wani abu yana tafiya gaba-gaɗi zuwa aji ko kuma shaƙatawa da kuma zamantakewa irin ta samartaka.

Irin mutane masu shekaru da mutum zai yi tunanin gani su ne farfesoshi da kuma malamai ba wai ɗalibai ba.

Sai dai a sakamakon yadda yanayin rayuwa yake sauyawa a duniya, wasu ɗalibai waɗanda ba yara ba ne suna amfani da shekarunsu domin neman ilimi a jami'a bayan sun yi ritaya.

A ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Ilimi Ta Duniya, BBC ta tattauna da wasu waɗanda suka kammala jami'a waɗanda ke da shekaru masu yawa daga ƙasashen Indonesia da Canada da Brazil da Indonesia domin gano dalilin da ya sa suke kallon neman ilimi a matsayin abin da ake yi tsawon rayuwa.

Brazil: 'Za mu iya taimakawa domin samar da al'umma mafi kyau'

Antonia Landgraf na da shekara 70, kuma ɗaliba ce.

Antonia dai na karɓar fansho kuma ta fito ne daga Nova Xavantina da ke tsakiyar Brazil wadda ke karatu a Jam'iar Mato Grosso.

"Bayan na yi ritaya daga aikina a bankin Brasil shekara goma da ta gabata, na kasa zama gida," kamar yadda ta shaida wa BBC.

"Mijina na kiwon shanu a gonarsa kuma ina so na taimaka masa. Sai dai koyon sabbin abubuwa na taimaka wa ƙwaƙalwata ta zama tana wani abu.

"Tun da farko na je na koyi ilimin tarihin ƙasa da kuma ƙididdiga," in ji ta.

Shekara goma da suka gabata kenan. Tuni ta koma ɓangaren noma.

A lokacin da ta shaida wa ƙawayenta cewa tana tunanin koma jami'a sai suka soma cewa ta soma haukacewa.

"Wasu sun ce ɓata lokaci ne, sai dai ina tunanin mutanen ƙarnin da na fito har yanzu akwai gudunmawar da za su iya bayarwa ga al'umma baki ɗaya."

"Ina ganin abu mai kyau ne mutum ya bar zuciyarsa a buɗe. Ba za a taɓa cewa an makara wajen koyon abu ba."

Sai dai komawa aji a shekarunta babban ƙalubale ne, kuma abin mamaki shi ne ita ce ta fi kowa shekaru a ajinsu.

"Na girmi har malamaina. Ga kuma ci gaban da aka samu ta ɓangaren kimiyya, ga manhajoji. A lokacin da aka shiga annobar korona, na yi ta fama da karatu ta intanet - a wani lokacin abu ne mai wahala na shiga aji ta intanet," in ji ta.

Sai dai daga baya duk ta saba da su.

"Ina jin daɗin abin da nake yi, da kuma ganin cewa wasu daga cikin abokaina sun yanke shawarar komawa jami'a."

Australia: 'Ilimi na sa mutum ya zama matashi'

Ruth Wilson mai shekara 88, ta kamma digirinta na uku a watan Fabrairun bata daga Jami'ar Sydney.

A wajenta "abu ne mai kyau da ma'ana", kuma mai cike da alfanu.

"Ilimi na ƙara maka ƙuruciya," in ji Dr Ruth.

"Kana koyon abubuwa da yawa da za su sake buɗe ƙwaƙwalwarka kan yadda rayuwa take a wannan zamanin. A ganina tamkar a rage shekaru 20 ne daga cikin naka."

Dattijuwar na da ƴaƴa huɗu da kuma jikoki biyar da tattaɓa kunni takwas, waɗanda shekarunsu suka kama daga wata shida zuwa shekara 12.

"Ƴaƴana sun ban goyon baya sosai - suna ganin abu ne mai kyau a ce na koma makaranta. Daya daga cikin ƴaƴana tana da digiri na uku kuma ta taimaka min wajen fahimtar yadda tsarin jami'a yake.

"Sannan ian da wata jika da ita ma take da digiri na uku - ta taimaka min wajen yin bincike da sauran ayyuka da suka shafi karatu.

"Komai ya zo min tamkar ban taɓa yi ba saboda rabona da karatu tun shekarar 1979, a lokacin da na kammala digiri na farko."

Canada: 'Har yanzu ina rubuta bayanin rayuwata'

Lois Kamenitz, mai shekara 70, ta so ta gano abin da ya sa tsofaffi ke komawa makaranta, don haka ta yanke shawarar yin hakan a karan kanta.

A farkon shekarar nan ta kammala digiri na uku daga Jami'ar York ta Kanada.

Ta yi bincike a kan mata masu shekaru 50 zuwa 60, sai ta gano cewa da yawansu, sun koma makaranta ne saboda jami'ar ta rage kuɗin karatun waɗanda suka manyanta.

Amma ita Lois, akwai wani abin mai muhimmanci ya sa ta komawar.

"Ni ce ta farko a gidanmu da na je jami'a. Don haka kafatanin hanyar da ka bi ka koma karatun sabo ne," ta cewa BBC.

A matsayinta nawacce iyayenta suka kasance ƴan cirani da ke aiki a masana'antu, iyayen ba su da ƙrfin da za su biya mata kuɗin ci gaba da karataun gaba da sakandare, amma sai ga shi bayan ta manyanta ta samu damar yin hakan.

Sannan kuma Lois na ganin kasancewarta mace ya sa wasu abubuwan da dama suna zama masu tsanani a gare ta.

Ta ce abin da ya sa ta yi wancan binciken shi ne don ta ƙaryata wannan kallon da mutane ke yi na cewa mutane ba za su iya komawa karatu ba idan sun manyanta.

Indonesia: 'Kar mu gaza wajen neman ilimi idan dai har muna fahimta'

Shekara biyu da suka gabata, La Ode Muhammad Sidik mai shekara 87, ya kammala karatu daga Jami'ar Muhammadiyah ta Buton, a tsibirin Sulawesi na Indonesia.

Mafarkinsa ne ya zamo gaskiya kamar yadda ya ce. Kuma yana da yaƙinin son ci gaba da karatu.

Tsohon malamin makarantar ya sha burin komawa jami'a, amma saboda nauyin iyali na ƴaƴa tara, dolensa ya haƙura da burikansa.

Amma a shekarar 2012, sai baban ɗansa ya ƙarfafa masa gwiwar komawa jami'a.

Shekararsa 78 a lokacin da ya koma. Amma shekararsa biyu da shiga kwaleji sai ya fara rashin lafiya.

"Na shafe shekara ɗaya da rabi ina jinya har sai da aka min tiyatar mafitsara," kamar yadda La Ode ya shaida wa BBC.

Sai dai duk da haka La Ode bai shirya haƙura da karatun ba, iyakansa sun ba shi goyon baya.

Lala, ɗaya daga cikin jikokin La Ode da ta raka kakan nata wajen taron yaye su, ta shaida wa kafafen yaɗa labaran ƙasar cewa kakanta bai taɓa ƙorafi kan karatun ba.

"Ko yaushe ya kan je aji, duk da cewa a lokuta da dama ba shi da lafiya, amma hakan bai hana shi zuwa makaranta ba," in ji Lala.

Bayan shekara bakwai, La Ode ya kammala digirinsa da taimakon ɗaya daga cikin tsoffin ɗalibansa, Nadir La Djamudi.

"Na gode musu sosai - na koya musu yadda za su zama nagari, su kuma sun taimaka min a lokacin da nake ƙoƙarin ƙaro ilimin."