Yadda tsofaffin hotuna suke tunawa 'yan Uganda zamanin iyaye da kakanninsu
- Marubuci, Daga Damian Zane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Ntare Guma Mbaho Mwine yana ƙoƙarin haɓaka ayyukan tsohon mai hoto marigayi Kibaate Aloysius Ssalongo, wanda ya dauki hotunan yadda mutanen ƙauyen Mbirizi suka yi rayuwarsu.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Rayuwa a lokacin da ake yin hotuna a kullum ana ajiye su a wayoyin hannu, za a iya manta ƙimar hotuna a zamanin da.
Hotunan zamanin da marasa kala, ka iya zama hanya ɗaya kacal da ra rage da wani zai gane dan uwa ko 'yar uwarsa da ya daɗe bai gani ba.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Wata rana mutane na rike lokacin da aka yi musu wani hoto saboda yiwuwar ɓacewar ainihin hoton shi kansa. Wani lokaci kuma hotunan kan lalace saboda tsawon lokaci.
Duk an tsakuro wadannan bangarorin na hotuna a cikin ayyukan Ssalongo.
Wani mai hoto mai suna Mwine, wanda aka haifa a Amurka amma asalinsa dan Uganda ne ya taba zuwa shagon daukar hoton Ssalongo a shekarar 1999. Motarsa ta baci a lokacin a Mbirize saboda haka yana da lokacin yin wasu abubuwa na daban.
An gayyace shi zuwa cikin shagon kuma dan Ugandan ya dauko masa wasu hotuna na zamanin da.
A cikin hotunan an ga wasu masu zama a kauyen a shekarar 1960.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
''Ya matukar burgeni saboda ayyukansa sun hadu sosai,'' a cewar Mwine a cikin shirin rediyo na BBC mai suna Focus on Africa.
Saboda nisan ƙauyen Mbirizi daga cikin birnin Kampala, "shi ne kadai a wannan shiyyar mai abin daukar hoto, saboda haka an san shi sosai a wurin. Kowa na son ya zo shagonsa a yi masa hoto."
Kuma mutanen da ake yi wa hoto yawancinsu mara sa galihu ne.
''Manoma da 'yan kasuwa ne yawancin wadanda ake yi wa hoton. Abin sha'awa ne ganin yadda wadannan mutane ke rayuwarsu kuma yadda suke gadara da aikinsu kuma yadda Ssalongo ke daukar hotunan yanayin mu'amalar mutane tsakaninsu.''

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Mwine ya zama abokin mai hoto Ssalongo kuma ya yi alkawarin haɓaka da kuma nuna wa duniya tsofaffin hotunansa.
Ssalongo ya rasa ransa a shekarar 2006 a lokacin da yake da shekara 67 amma shirin nasa ya ci gaba. Shirin mai suna Memories of Love Returned, ya nuna hotuna akalla 5.000 a karo na farko a Mbirizi.

Asalin hoton, Mwine
Kwalin mai dauke da hotunan ya kai tsawon mita 100 kuma mutane daga wurare daban-daban a kauyen sun zo kallon hotunan domin ganin ko za su ga kansu ko wasu 'yan uwansu.
"Hakan ya bayar da damar tuna abubuwan da suka faru a da wadanda mutane suka manta," in ji Mwine.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Wani wanda ya zo kallon baje kolin mai suna Johnson Makanga ya ce bai san kamannin mahaifinsa ba saboda ko da ya rasu yana yaro.
Amma dan uwan mahaifin nasa ya ga hoton mahaifin a baje kolin wanda ya kuma nuna mahaifiyar Jonhson da gwaggwonsa.
"Johnson ya ji dadi sosai saboda a lokacin ne karo na farko da ya ga kamannin mahaifinsa."
Sai ya ji wani jimami ya taso masa amma duk da haka ya kuma ji dadi sosai saboda "ya ga kansa a cikin fuskar mahaifinsa."
Wasu maza su biyu, 'yan uwan juna masu suna Kukumba Emmanuel da Katerega Isaac Muguzi su ma sun ga hoton mahaifinsu wanda ya yi aiki a matsayin dan majalisa a kauyen kuma an yi hoton a shekarar 1962.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Lubyayi Martin Onesmus Muguzi shi ne dan majalisa na farko a karamar hukumar Lwengo wanda kauyen Mbirizi ke karkashinsa.
Hoto na farkon an dauke shi ne a ranar da Muguzi ya samu albashinsa na farko bayan da ya samu mukamin.
Yaransa maza sun yi mamakin ganin mahaifinsu a matsayin yaro a cewar Mwine.
Kuma Nalongo Tedddy ta ga hoton aurenta wanda ta dade tana nema shekaru 40 da suka wuce.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Ta kuma ga hoton 'yarta wacce ta je shagon hoton da ita. Ba ta da isashen kudin sayen hoton a lokacin.
Kamar yadda aka yi wa sauran mutane da suka ga kansu ko wanda suka sani a baje kolin hotunan. Mwine ya ɓata hotonta domin ta tafi gida da shi.
Yayin da mutane suka ta kallon hotunan, Mwine ya ga yadda mutane suka tsunduma tuna zamanin da.
''Wata rana mutane za su iya rasa rayukansu kuma shikenan an manta da su, saboda haka abinda ya sa na fi jin dadi shi ne mutane sun tuna abubuwa kuma hakan ya sani farin ciki.''
A cikin shekarun baya Mwine da kansa ya yi wa mutane a kauyen hotuna domin kara daukar wasu hotunan Ssalongo.

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine

Asalin hoton, Ssalongo/Mwine
Ya kai aikin Ssalongo zuwa Mbirizi saboda ya sama wuri na farko da aka ganshi amma yanzu yana so ya kai ayyukan nasa zuwa kasashen waje. Yana kuma da burin rubuta litttafi da fim mai dogon zango.
Mutane a Nahiyar Turai da Amurka suna yi wa hoto wani kallo na daban amma Mwine yana fatan cewa hotunan Ssalongo za su ''nuna wa mutane soyayya da mu'ammala kamar yadda ba a taba gani ba.''
''Wadannnan hotunan masu nuna mu'amalar mutane sun saba bacewa a duk lokacin da ake nuna bayyana tarihin Uganda.''

Asalin hoton, Mwine









