Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa China za ta iya kere kasashen duniya wajen mallakar makamai
- Marubuci, Daga David Brown
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
- An wallafa
China na gaggawar kafa rundunar soji mafi karfi a duniya cikin sauri.
Ta kara bunkasa fasahar makamai masu linzami, da makaman nukiliya, da basirar na'ura sun janyo damuwa ga kasashen yammacin duniya, wadanda suka yi amanna da cewa nan gaba kadan kasar za ta karfafa sojojinta fiye da kowacce kasa a duniya.
Shugaba Xi ya bai wa sojojin China umarnin sake fasalin rundunar da zamanantar da ita nan da shekarar 2030. Ya ce su tabbatar sun zarce takwarorinsu na duniya, ta hanyar yaki da yin nasara daga nan zuwa shekarar 2049.
Wannan gagarumin yunkuri ne, amma babu wata kasa da ake takalar fada.
Kashe kudi
Masu sharhi na kasashen waje na sukar China kan kunbiya-kunbiya, da kin bayyana adadin kudaden da za ta kashe wajen bunkasa tsaron kasarta, da kuma adadin abin da za a kara na samun nasarar.
Beijing dai na wallafa kididdigar kudaden da gwamnati ke kashewa. Amma kididdigar da kasashen yamma ke da ita na kudin da take kashewa na bunkasa tsaronta ya zarce wanda ake gani a zahiri.
An yi amanna da cewa a halin da ake ciki baya ga Amurka, China ce kekashe makudan kudade wajen bunkasa sojinta a duniya.
Karuwar kasafin kudin rundunar sojin China ya sha gaban tattalin arzikin ta na shekaru 10 da suka gabata, kamar yadda cibiyar bincike da kididdiga ta Washington ta bayyana.
Bunkasa kera makaman nukiliya
A watan Nuwamba, ma'aikatar tsaron Amurka ta yi hasashen China na kokarin bunkasa makamin nukiliyarta da kashi uku daga nan zuwa karshen 2030. "Akwai alamun China za ta samar da kwanson nukiliya 1000 kafin shekarar 2030".
Kafar yada labaran China ta kira ikirarin da ba shi da tushe bare makama, tare da cewa karawa ko bunkasar makaman nukiliya bai kai inda ake magana ba, zuzutawa ake yi.
Haka kuma, kwararru a cibiyar binciken kasa da kasa ta Stockholm, ta wallafa rahoton ta na shekara-shekara kan yadda ake bunkasa kwanson nukiliya, ya nuna cikin shekarun nan China ta kara bunkasa kwanson makaman nukiliyarta.
Amurka ta sha gaban China wajen adana kwanson makaman nukiliyarta a rumbun ajiya, inda ta ke da kwanson guda 5,550, sai dai ana ganin bunkasa makaman nukiliyar kasar babbar barazanar ce ga kasashen yamma.
"Makaman nukiliyar China su ne batu mafi mihimmanci," kamar yadda Veerle Nouwens, na cibiyar bincike ta Royal United Services da ke Landan ya bayyana.
"Akwai gagarumin rashin yadda daga bangarorin biyu, kuma kin amincewa sasantawar alamu ne da ke nuna dukkan bangarorin ba sa bukatar hakan. Ga kuma karuwar fargaba kan hadarin da ake ciki."
Makomar makamai ma su cin dogon zango
Makamai masu linzami da ke cin dogon zango, na tafiya mai karfi sau biyar idan aka kwatanta da karar da ake ji.
Gudun su bai kai kananan makamai masu linzami da ke tafiya kamar kiftawar ido ba, suna da wuyar ganowa ko da a cikin jirgi ne, suna samun kariya daga iska.
"China ta gano an dade da barinsu a baya, don haka suke kokarin gaggauta bunkasa nasu cikin sauri da fatan su wuce sauran kasashe," Kamar yadda Dr Zeno Leoni, na kwalejin King's da ke birnin Landan ya bayyana.
"Abin da suke kokarin yi a yanzu shi ne bunkasa makamai masu karfi da cin dogon zango."
Sai dai China ta musanta gwajin makaman masu linzamin, amma kwararru sun yi amanna da cewa an yi gwajin makaman roka sau biyu a lokacin bazara, sun nuna sojojin sun shirya tsaf kuma su na kan hanyar cimma burin da kasar ke da shi.
Sai dai babu tabbacin salon da China ke amfani da su wajen bunkasar makamanta. Akwai dai abubuwa guda biyu:
- Hypersonic glide missiles; Shi ne makami mai linzamin da ke tsayawaa sararin samaniya
- Fractional orbital bombardment; Shi ne makami mai tafiya a hankali, kafin daga bisani ya dunfaru inda aka dana shi.
Kuma ta yiwu China ta yi nasarar samar da duka biyun da kuma harba su a lokaci guda.
Dr Leoni ya ce yayin da makami mai linzami samfurin hypersonic ka iya kasancewa ba shi zai sauya tsarin China na kera makaman ba, za su iya zama wadanda za a yi amfani da su domin cimma wata bukata.
"Su jiragen da ke daukar makami mai linzamin na da matukar wuyar karesu," In ji shi.
Fasahar kirkira da kutse ta intanet
Ma'aikatar tsaro a Amurka, ta ce China ta maida hankali kan bunkasa fasahar yaki a zamanance, da makomar sojojinta, da fargabar shigowar fasaha, musamman fasahar kirkira.
Makarantar horas da sojoji mai amfani da kimiyya ta China, an ba ta umarnin sanya hakan cikin wani salo na horas da sojojin, a wani fannin kuma kamfanonin fasahar China masu zaman kansu na aiki tare da ma'aikatar tsaron kasar.
Tuni China ta gudanar da ku kutse ta intanet mafi girma a duniya, kamar yadda kwararru suka bayyana.
A watan Yuli kassahen Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai suka zargi China da kaddamar da kutse ta internet mafi girma ta hanyar amfani da manhajar musayar bayanai ta Microsoft.
Sun yi amanna da kutsen ya shafi akalla kungiyoyi da kamfanoni 30,000 a fadin duniya, kuma an yi nufin kwashe bayanan fitattun mutane, da manyan 'yan boko da kamfanonin da sauransu.
Kasa mai karfin sojin ruwa
China ta sha gaban Amurka a karfin sojin ruwa a duniya, sai dai kwararru sun ce yawan jiragen ruwan kasa ba dalili ne da ke nuna kasa ta bunkasa har ta fi karfin kowacce kasa ta fannin sojojin dare.
Sai dai sun ce, gwaji da kayan aiki abin, na da muhimmanci.
A halin yanzu, Amurka tana da karfi a sojan ruwa, inda take da jirage sama guda 11 yayin da China ke da guda biyu, da manyan jiragen ruwa na yaƙi.
Amma ana sa ran China za ta faɗaɗa ƙarfin sojan ruwanta.
Tsohon babban sojan China Kanal Zhou Bo, na Jami'ar Tsinghua a Beijing, ya ce yana ganin abu ne "mai matuƙar muhimmanci" ga China ta ƙarfafa sojan ruwanta domin magance duk wata barazana da take fuskanta.
A takaici, ya ce: "Babban matsalar da muke fuskanta shi ne tunanin takalar Amurka a ruwan China."
Rundunar sojnan ruwan China ta ce tsakanin 2020 zuwa 2040, yawan jiragen ruwan China zai su ƙaru da kusan kashi 40.
Makoma mara tabbas
Shin kasar China tana sauya matsayi ne zuwa wani matsayi mai barazana?
A halin yanzu, tsarin kasar China har yanzu yana "nasara ba tare da faɗa ba", in ji Dokta Leoni, ko da yake ya kara da cewa zai iya canza wannan dabarar nan gaba.
"Kasancewa cikakken ingantaccen ƙarfin sojan ruwa zai iya zama wani babban mataki."
Sai dai babban Kanar Zhou ya jaddada cewa fargabar kasashen yammacin duniya ba ta da tushe.
"China ba ta wata niyya na yi wa duniya barazana, saɓanin Amurka," in ji shi. "Ko da China ta zama mafi ƙarfi wata rana, zat a mutunta tsarinta.
China ba yi yaƙi ba tun 1979, lokacin da ta yi yaƙin Vietnam, ba ta gwad ƙarfin sojinta ba a yanzu
Da dama a yammaci da China na fatan hakan zai ci gaba da kasancewa.