Me yake yawan jawo munanan guguwar da Amurka ke fama da ita?

    • Marubuci, Daga Jake Horton and Esme Stallard
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
  • An wallafa

Jihohin Amurka da dama sun fuskanci mummunar guguwa, inda ake sa ran adadin wadanda suka mutu ya haura 100.

Waɗannan ba kasafai ake samu ba lokacin bazara da rani a Amurka, amma a wannan watan na Disamba barazanar guguwa ta ƙaru.

Don haka sauyin yanayi na haddasa guguwa kuma mai ƙarfi.

Ta ya ake samun guguwa?

Lokacin da iska mai ɗumi ta haɗu da iska mai sanyi, tana haddasa tsawa. Iskar mai ɗumi za ta ƙaru, kuma ta ci gaba da ƙaruwa.

Kuma idan akwai iska mai ƙarfi da ke kaɗawa ta hanyoyi da dama, iskar za ta fara juyawa.

Ƙaruwar iska mai ɗumi za ta ci gaba kuma har zuwa haifar da tsawa. Kuma da zarar ta taɓa ƙasa za a samu guguwa.

An fi samun iska mai ɗumi a lokacin watannin zafi.

Girman guguwar da aka samu a watan Disamba ba a cika samu ba a Amurka.

Guguwa ta zama ruwan dare?

An samu guguwa a shekaru 20 da suka gabata fiye da shekaru 20 baya - amma wannan saboda ƙoƙarin da aka yi na taƙaitawa.

An samu ci gaba na tattara alƙalumma, kuma ba a samu guguwa ba akai akai.

"Ga waɗanda ba su fahimta ba, za su ga kamar muna yawan samun wannan al'amari - amma gaskiyar abin da ke faruwa shi ne muna da na'urori da dama na gane guguwa mai rauni," in ji Jana Houser, Farfesar yanayi a Jami'ar Ohio.

Amma nau'in guguwa - lokacin shida ko fiye suka fara cikin sa'a shida tsakaninsu - abu ne mai faruwa.

Ko da yake akwai kwanaki kaɗan na guguwar - matsakaici kusan 100 zuwa 150 a 1970 - an fi samun guguwa a lokacin.

Akwai alaƙa da sauyin yanayi?

Babu wani al'amari na yanayi da za a alaƙanta da sauyin yanayi.

Amma yawaitar guguwa "ya nuna yanayin ya sauya," kamar yadda masanin yanayi Harold Brooks na NOAA ya bayyana.

"Wannan zai iya faruwa saboda sauyin yanayi - amma ba za mu iya yanke hukunci ba," a cewarsa.

Yanayi mai zafi na ƙara zafafa yanayi da kuma yiyuwar yin ɓarna.

Amma "akwai babu wata matsaya ta kimiya" kan guguwa, in ji Mista Brooks

"Ba wai matsaya kan ƙaruwar zafi ba ko ruwan sama mai ƙarfi ba."

Gudu da ƙarfin iska su ne manyan abubuwan da ke tasiri wajen haddasa guguwa - amma akwai ƙarancin hujjoji kan yadda za su sauya saboda ɗumamar yanayi.

A lokacin da yake jawabi bayan guguwar da aka samu, Shugaban Amurka Joe Biden ya ce "zai tambayi hukumar kare muhalli da sauransu domin nazari kan (rawar da sauyin yanayi yake takawa).

"Gaskiyar ita ce mun san komi ya fi tsauri idan sauyin yanayi na ɗumama, in ji shi.

A 2018, kwamitin gwamnatoci kan sauyin yanayi ya gano cewa "yanayin da ya dace da guguwa kamar gurɓacewar yanayi zai ƙaru saboda ƙaruwar zafi da ɗumamar yanayi."

Amma sauran yanayin da zai iya rage samuwar guguwa shi ma akwai shi.

Shin guguwa tana ƙara tsananta ne?

Babu wata hajja da ke nuna cewa guguwa na ƙara girma, a cewar wani bincike na cibiyar nazarin yanayi.

Mafi muni a cikin guguwar da aka samu a ƙarshen wannan mako da ake kira jihohin Quad - katsewar Arkansas da Missouri da Tennessee da Kentucky.

Ba gudun iskar ba ce, ko da yake, ta kasance wadda ba a taɓa gani ba amma girmanta ne.

An ba da rahoton cewa za ta iya gudun mil 220 - fiye da nisan tazarar da ke tsakanin London zuwa Paris.

Shin yankin da ke da girma ya fi fuskantar hatsari?

An fi samun guguwa a mashigin tsakiyar Amurka da ake kira Tornado Alley.

Wannan ya haɗa Texas da Louisiana da Arkansas da Oklahoma da Kansas da South Dakota da Iowa da Nebraska.

Amma wasu hujjoji sun nuna sauyin guguwar zuwa kudancin Amurka.

Mista Brooks ya ce: "Tornado Ally ba a fayyace ta ba, wannan wani abu ne mai wahala da za a iya faɗa.

"Mun ga ƙaruwar guguwa da kusan kashi 10 a shekaru 40 a yankin tsakiyar kudancin da kuma raguwa a yankunan Texas da Kansas.

Ta sauya - amma ba wani babba ba."