Shugabancin APC a Kano: Mutum biyu da zani daya

    • Marubuci, Ibrahim Isa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da irin rikicin da ya dabaibaye zaben shugabanni na jihar Kano a arewacin ƙasar da aka gudanar ranar 12 ga watan Oktoban 2021 za iya cewa tamkar mace da ciki ce, wadda ba a san abin da za ta haifa ba.

Rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamnan jihar, Senata Ibrahim Shekarau da wadansu jiga-jigan jam'iyyar, wanda har wa yau ƴan majalisar dattawa da majalisar wakilai ne daga jihar ta Kano ya yi ƙamari har ta kai ga haddasa rarrabuwar kai a zaben shugabanni na jihar da aka gudanar.

Kuma wannan lamarin ya yi sanadin ɓaraka a jam'iyyar ta APC a jihar, inda aka samu ɓangarori biyu da suka yi hannun-riga wajen gudanar da zaɓen.

Wato tsagin Gwamna Ganduja ya keɓe a zauren wasanni na Sani Abatcha da ke birnin Kano, yayin da tsagin Shekarau kuma ya yi nasa taro a unguwar Jan-guza.

Yanzu dai ana da shugabannin jam'iyyar APC biyu a Kano. Abdullahi Abbas na tsagin Ganduje da kuma Ahmadu Haruna Zago na tsagin Shekarau.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntubar bangarorin biyun don jin irin zaman da za a yi, amma ba ta yi nasarar samun wani daga cikin shugabannin tsagin Ganduje ba.

Amma wani jigo a bangaren, kwamishinan raya karkara, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce dole a bi zabin da gwamna ya yi.

"Gwamna shi ne yake fitar da shugaban jam'iyya. Kuma duk abin da ya fada shi ne yake tabbata.

"Haka Malam Ibrahim Shekarau ya dauko Salisu Sagir Takai a matsayin dan takarar gwamna aka haƙura, aka ce duk abin da Malam ya ce daidai ne.

"Kuma yanzu don gwamna ya zo ya ce Abdullahi Abbas ne shugaban jam'iyya, an je an yi zabe kowa na gani sai a ce ba haka ba?" in ji Musa Iliyasu Kwankwaso.

Amma shugaban bangaren Shekarau, Alhaji Haruna Ahmadu Zago ya ce babu abin da zai hana shugabanni biyu su yi zamaninsu a lokaci daya, saboda "ba sabon abu ba ne wannan.

"Abun da ba a yi biyu shi ne gwamna. Amma shugabancin jam'iyya ana iya yin shugabanni uku ma, kowa ya ji da mutanensa."

Tushen Rikicin

Tun bayan zaben shugabannin majalisar kananan hukumomi da zabukan shugabannin jam'iyyar APC na gundumomi da kananan hukumomi ake yi wa ƴan tsagin Shekarau, laƙabi da 'ƴan bakwai'.

Mutanen sun haɗa da Senata Kabiru Ibrahim Gaya (kodayake daga baya ya fice daga wannan tafiyar) da Senata Barau Jibrin da Hon. Sha'aban Ibrahim Sharada da Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe da wasu suka yi zargin cewa ana mai da su saniyar-ware, saboda ba a tuntuɓar su ballantana ma a ba su wani kaso daga cikin waɗannan muƙaman.

Kenan ana kokarin kwashe musu ƙafa ne a zaben shekara ta 2023. Wannan ne ya sa suka rubuta takardar korafi ga hedikwatar jam'iyyar APC suna sukar yadda zabukan suka gudana tare da jaddada cewa ba za su amince da su ba.

Ƴan Magana dai sukan ce abokin kuka ba a boye masa mutuwa. Sannu-sannu, haka wannan gangami na Ƴan bakwai ya ci gaba da tuntubar masu irin nasa ra'ayin har a karshe suka ware suka yi nasu zaben shugabannin jam'iyyar APC na jihar Kano, inda Alhaji Ahamdu Haruna Zago ya zama shugaba.

A bangaren Gwamna Ganduje kuma, Alhaji Abdullahi Abbas aka zaɓa a matsayin shugaba, kuma tuni kowane tsagi ya rantsar da nasa shugaban.

Tsagin Ganduje dai ya ce zaben da ya gudanar shi ne na kwarai saboda kwamitin da hedikwatar jam'iyyar ta tura jihar shi ne ya sa ido a kan zaben.

Amma tsagin Shekarau shi ma yana ikirarin cewa shi ma Ƴan kwamitin hedikwatar jam'iyyar APC ne suka je wurin nasa zaben.

Hon. Sha'aban Ibrahim Sharada ya ce "cikin mutum bakwai da jam'iyyar ta tura su gudanar da zaben nan, uku daga ciki suka zo suka shaida zabenmu, kuma suka rubuta."

BBC ta yi kokarin tuntubar shugaban tsagin Ganduje, Abdullahi Abbas game da zargin cewa ba a tuntubar ƴan tsagin Shekarau a zabukan da suka gabata, amma ba ta yi nasara ba.

Sai dai kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya musanta. Ya ce "wadanda suka taho da mai girma Sardauna (Malam Shekarau) duka an ba su muƙami.

"Akwai PRO na jam'iyya, Ahmed Aruwa da mai bai wa jam'iyyar shawara a bangaren shari'a, Barista Abdul duka ƴan gidan Sardauna ne."

Yayin da ake kokarin neman hanyar kashe wutar rikicin, wani abin da ya rura wutarsa shi ne matsayin da kwamitin da hedikwatar jam'iyyar APC ta tura Kano domin sauraron ƙorafin zaben a karkashin jagorancin Mista Tony Macfoy.

Shi ne wanda ya ce ba shi da hurumin sauraron kowa sai wanda ya yi zabe a filin wasa na Sani Abacha, inda tsagin Gwamna Ganduje ya yi nasa zaben.

Wannan ya sa wadansu rade-radin cewa hedikwatar jam'iyyar APC ta karkata ga bangaren tsagin Ganduje kenan.

Rikicin zai yi babbar illa ga APC a Kano da zaben 2023- Farfesa Kamilu Fagge, masanin kimiyyar siyasa na ganin cewa rikicin shugabannin da ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Kano zai iya kai jam'iyyar kasa, idan ba a dauki matakin shawo kan lamarin ba.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, "jihohi akalla 13 ne suke fama da irin wannan matsala ta darewar jam'iyyar APC a Najeriya. A wani wurin ma ana da tsagi fiye da biyu. Mu nan Kano akwai zafin aƙida na siyasa.

Karin wasu labaran da za ku so

A baya ma an samu irin haka

A baya an samu irin wannan rarrabuwar kai a jam'iyyar PRP inda aka samu santsi da tabo. Kuma wannan ne yake tasiri a yanzu.

Idan ba a dinke barakar ba, akwai hadari saboda za ta yi wa jam'iyyar babbar illa. Idan rikicin ya ki ci ya ki cinyewa to wasu za su fice daga jam'iyyar.

Wadansu kuma ko ba su fita ba, za su tsaya su yi mata kafar-ungulu.

Kamar yadda ta kasance a zaben shekara ta 2015, inda wadansu suka fita daga PDP, wadansu kuma suka tsaya suka yi wa jam'iyyar zagon-kasa, "mafita kawai" in ji Farfesa Kamilu Fagge ``ita ce uwar jam`iyyar APC.

Kamata ya yi kwamitin da ta kafa na sulhu ya saurari kowane bangare domin ya daidaita su."

Masanin ya bayyana cewa irin wannan turka-turkar na zubar da kima ko martabar jihar Kano, wadda a baya jihohi, musamman a arewacin kasar suke mata kallon abin koyi a fagen siyasa.

Matsayin hedikwatar APC

Sabanin rade-radin da ake yayatawa game da bangaren da hedikwatar APC ta karkata dangane da rikicin shugabancin ƴaƴanta a Kano, wata majiya mai karfi ta tabbatar wa BBC cewa har yanzu uwar jam'iyyar ba ta yanke shawara a kan abin da yake faruwa ba, sai ta kammala tattara rahotanni daga sassan Najeriya baki daya.

Shi ma kwamitin sulhun da ta kafa, a halin da ake ciki yana tsara hanyoyin da zai bi ne wajen kaiwa ga ƴaƴan jam'iyyar don sasanta tsakaninsu.

Ƴaƴan jam'iyyar APC da dama dai sun zuba ido su ga yadda lamarin zai kaya. Kodayake da tsagin Ganduje da na Shekarau dai, duka sun nuna cewa a shirye suke su hau teburin sulhu!