Shin jarabar shaƙuwa da intanet ta zama babbar matsala ce?

    • Marubuci, Daga Nick Dauk
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
  • An wallafa

Cam Adair ya fahimci cewa sabon da ya yiwa wasannin hotuna masu motsi na bidiyo wato Video games ya wuce hankali, a lokacin da ya yanke shawarar kashe kansa.

"Na shafe shekara 10 ina fama da damuwa" a cewarsa, "na bar makaranta, na kuma yi karya a gidanmu cewa ai ina aiki."

"A karshe na rubuta wasika na fadi cewa zan kashe kaina, kuma a wannan daren ne na fahimci cewa ina bukatar taimako. A yanzu na shafe kwanaki 3,860 da rabuwa da mugun sabon da na yi wa wasannin video games."

Mr Adair dan shekara 32 daga Canada, kuma a halin yanzu shine shugaban kungiyar wadanda suka raba gari da buga wasannin video games, wadda ke taimaka wa wadanda video games suka zame wa jiki.

Maganar da ake a halin yanzu wannan kungiya na da mambobi 75,000 a fadin duniya.

Duk da cewa fasaha musamman intanet ta taimaka mutane a lokacin kullen korona, a cewar Adair ta zama matsala ne ga mutane irinsu.

"A lokacin annobar na kan shafe lokaci mai tsawo babu abinda nake sai kallon shirin 'Twitch', wani shiri da ya maida hankali kan masu sha'awar gyam din kwamfuta. Sannan kuma na kan kalli Youtube."

"Ko a Youtube din abubuwan da nake kallo suna da alaka da video games, kuma dama irin wadannan abubuwa ne ke sa ka yi wa video games mugun sabo kuma ko ka daina sai ka koma ruwa."

Sai dai a yanzu matashin ya ce ya kan iya dakewa baya tunanin komawa ruwa, amma ya san a kungiyarsu ma akwai wadanda sun koa ruwa da aka shiga kullen korona.

Hukumar magani ta Amurka ta saka mugun sabon a matsayin daya daga cikin cutukan da suka shafi sabo da intanet.

Hukumar ta bayyana shi a matsayin wani yanayi na sabo da kwamfyuta ta intanet da ya wuce kima, wanda ka iya haifar da matsalar ido da kuma rashin natsuwa.

Duk da cewa wasu za suce ai ba cuta ce mai hadari ba kamar shan giya ko shan miyagun kwayoyi, matsala ce mai hadari da ka iya mummunar illa kan masu fama da ita.

Dr Andrew Doan likitan kwakwalwa ne kuma masani kan cutar mugun sabo da intanet, kuma ya tabbatar da cewa kullen korona ya ta'azzara matsalar.

"Annobar korona ta kara sa wa mutane damuwar da wasu ba ta gushe musu idan har ba su nishadantu da intanet ba, kamar buga video game ko kuma shiga shafukan sada zumunta."

"Kuma a irin haka ne amfani da intanet din zai zame musu jiki ba tare da sun sani ba."

Sai dai akwai wasu kamfanonin da ke samar da video games da suka bullo da hanyar da iyaye za su rika sa ido kan yadda 'ya'yansu ke amfani da intanet don gudun kar ta zame musu jiki.

Linewize na daya daga cikin wadannan kamfanoni da ke da manhajar da ke ba iyaye damar sanin tsawon lokacin da 'ya'yansu suka shafe akan intanet.

Hakama Linewize na da wani makulli da ke rufe hotunan batsa ko wasu abubuwa da basu dace yaran su gani ba a intanet.

Teodora Pavkvic kwararriya ce kan ilimin halayyar dan adam da ke aiki a ofishin Linewise da ke San Diego, ta kuma ce yi wa intanet mugun sabo ba abu ne mai wahala ba a tsakanin matasa, musamman yan kasa da shekara 25."

"Ta kara da cewa an samar da intanet ne don a bata mana lokaci a kuma ja hankalinmu ta amfani da wasu abubuwa da ka iya saurin shiga ranmu mu yi sabon da ya wuce kima."

"Kuma cikin sauki za a iya cin galaba kan matasa da ke saurin shakuwa da abubuwan nishadi." inji ta.

Ga manya kuma masana sun gano cewa intanet na zame musu jiki ne ta hanyar manhajojin caca.

Don magance matsalar mugun sabo da caca ne BetBlocker ta bullo da wata manhaja da ke toshe wa dubbai damar amfani da shafukan caca na wani lokaci.

Matsawar aka dakatar da mutun ba zai iya yin caca ba har sai lokacin da dakatarwar ta daina aiki.

Shima Dr Doan masani ne kan video games wanda a baya ya samu matsalar mugun shakuwa da wasannin.

"A lokacin da nake karatu a jami'ar Johns Hopkins ina shafe awa 80 zuwa 100 ina buga game a kowa ne mako har tsawon shekara 10," in ji Dr Doan.

Abun da na ke fargaba shine irin lokacin da muke shafewa a intanet akwai yiyuwar mu fuskanci matsalar mugun sabo da ita.

Duk da haka, Cam Adair na fatan kamfanoni kamar Linewize, da BetBlocker da GameBlock za su taka rawa ta musamman wurin magance matsalar sabon da ya wuce hankali da ake yi wa intanet.

Kuma yana ganin abu ne mai muhimmanci duk wanda ya samu kansa a irin wannan yanayi ya yi kokarin ganawa da likita.

An wallafa aikin da Mr Adair ya yi a wata makala da aka yi kan cutar tabin hankali, kuma yanzu ya zama wata murya a duniya da ke tattaunwa batun mugun sabo.

"Abin da ya tseratar da rayuwata shine neman taimako da na yi. Na shiga matukar damuwa, na kebe kaina ba na shiga jama'a kuma bana bari wani ya kusance ni a lokacin.

"Amma yanzu ian cikin farin ciki kuma ina iya yin rayuwata ba tare da barin wani abin duniya ya zame mani jiki ba."